Masu kiwon kaji a Legas sun nuna damuwarsu kan raguwar cinikin kwai, inda suka danganta hakan da matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashin kayayyaki.
Shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji ta jihar Legas, Mista Mojeed Iyiola, ya bayyana cewa ko da yake ƙwai na ɗaya daga cikin mafi arha cikin abinci mai gina jiki, yawancin al’umma ba sa iya siye saboda talauci.
- Dole Ne Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samar Da Ayyukan Yi Da Rage Talauci — Bankin Duniya
- Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
“Farashin ƙwai yana kai wa N5,500 a gidan kaji, amma idan ya kai kasuwa ya hau har N6,500. Matsin tattalin arziƙi sun sa mutane suka ƙauracewa siyan kwai,” in ji Iyiola.
Mista Joel Oduware, wani dillalin kaji, ya ƙara da cewa ko da makarantu sun buɗe, amma sayar da ƙwai ya ragu musamman a yankunan Arewa.
“Don guje wa asara, masu kiwon kaji za su yi la’akari da rage farashin, amma hakan na dogara ne kan rage farashin kayayyakin da ake amfani da su,” in ji Oduware.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp