A wani rahoton da ta fitar a makon da ya gabata, hukumar samar da abinci ta duniya wato, WFP ta ce yunwa za ta tsananta a shekarar 2022 a Nijeriya sakamakon karuwar hare-haren ‘yan bindiga musamman a Arewacin kasar nan.
Bugu da kari, rahoton ya ce fiye da mutum miliyan 31 a yankin yammacin Afirka za su fuskanci barazanar yunwa sakamakon tsadar kayan abinci da kuma rikici da matsaloli na tsaro.
A cewar rahoton farashin abinci ya ninka da sama da kashi 200 a kasashen yammacin Afirka, wanda ya jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali na samun abin da za su kai baka, sakamakon matakan da annobar korona ta tilasta aka dauka na tattalin arziki.
Rashin noman zai kara haifar da karancin abinci da kuma tsadarsa, kamar yadda yin noma zai samar da abinci da rahusa.
Bisa ga alkaluman da hukumar kdiddiga ta kasa ta fitar a watan Fabarairu sun nuna cewa, an samu hauhauwar farashin da ya kai kashi 17.33 cikin dari a watan Fabrairu da ya wuce, inda kuma alkaluman suka nuna cewa tashin farashin ya karu da kashi 1.54 a watan Fabarairun 2022, idan aka kwatanta da kashi 1.49 a watan Janairu.
.
Har Ila yau, farashin kayan abinci ya tashi da kashi 21.79 a Fabarairun da ya gabata, idan aka kwatanta da kashi 20.57 a watan Janairu.
Hukumar ta ce, wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashi a cikin shekaru hudu da suka wuce.
Bugu da kari, a yayin da daminar bana ta kankama an kuma ci gaba da fuskantar tsadar kayan abinci da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane, al’amarin da ya jefa manoma a arewacin kasar nan a cikin matsala, inda musamman abin ya fi shafar manoman da ke karkara, inda matsalar ta janyo koma-baya noma da kuma kara janyo samun kudaden shiga ga manoma.
Hare-haren ‘yan bindiga da masu fashin-daji a kauyukan jihohin arewa maso yammacin kasar nan musamman Zamfara da Katsina da yankin Birnin Gwari a Kaduna sai kara munana yake yi.
Manoma da dama a wadannan jihohin, tuni suka hakura da manyan gonakinsu da ke a kauyukansu inda suke ci gaba da jin tsoron koma wa don su ci gaba da yin noman.
Rashin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali musamman a jihohin Arewa maso yammacin kasar nan ya sa har yanzu manoman da suka yi gudun hijira ba su koma gonakinsu ba, matakin da ya rage yawan abincin da ake samarwa a kasar nan.
Wasu manoma ‘yan gudun hijira daga jihar Zamfara sun bayyana cewa kafin su yi gudu hijira suna noma sosai wanda suke ciyar da iyalinsu har su kai kasuwa su sayar, amma yanzu ba sa da halin yin noman.
A cewarsu, ‘yan fashin-daji sun hana su sakat, inda hakan ya tilasata suke arece wa don su tsira da rayukansu, inda suka bayyana cewa za a shafe shekaru goma a jihar kafin noma ya dawo daidai saboda a cewarsa noman gaske da aka sani a Zamfara ya gagara, saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Wasu masana a fannin aikin noma a kasar nan sun yi hasashen cewa, zai yi wuya a noma amfanin gonar da aka saba samu nan da sama da shekaru goma masu zuwa, musamman a jihohin da matsalar ta fi ta’azzara, in har makunta a kasar nan, ba su gaggauta lalubo da mafita ba.
Har ila yau, masanan sun yi nuni da cewa, rashin tsaro da kwanciyar hankali ga manoman wata babbar barazana ce ga wadatar abinci a kasar nan, musamman a arewacin kasar nan.
Sun sanar da cewa, hauhawar farashin kayayyaki masarufi a kasar nan na ci gaba da yi wa tattalin arziki Nijeriya illa haka wasu masana a fannin arzikin tattalin arzikin kasar nan, inda kuma faduwar darajar naira,
Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ake hasashen za su haddasa karancin abinci a arewacin Nijeriya saboda yadda ‘yan fashin-daji da masu garkuwa ke addabar manoma suna hana su nome gonakinsu.
Ana ganin kalunbalen tsaro da manoma ke fuskanta zai yi tasiri ga samar da abinci a Nijeriya.
Masanan sun kara da cewa misalia wasu yankunan Katsina suna noma abinci kusan kashi 30 zuwa 35 na abin da ake samu a arewa maso yamma gaba daya, sai dai a yanzu noman zai gagara, manoma za su kasa zuwa gona, inda suka bayyana cewa, wannan matsala suka ce za ta haifar da tsadar kayayyakin abinci a yankin arewacin Nijeriya saboda rashin abincin.