Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba bukatar gaggawa ta batun sake bude iyakokin Nijeriya domin shigo da kayan abinci daga kasashen waje domin ragewa al’ummar Nijeriya radadin tsadar rayuwa.
A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya roki wannan bukatar ne jim kadan bayan ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam na Nijeriya, Alhaji Bashir Adewale Adeniyi a gidan gwamnati da ke Kano.
Gwamnan ya koka da halin matsin tattalin arziki da yunwa da ake fama da shi a kasar nan sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp