Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba kayan abinci da sauran kayan agaji ga mazauna unguwar Feezan da ke birnin Maiduguri 2,000.
Rabon tallafin da aka gudanar a ranar Laraba a kwalejin koyon shari’a da addinin musulunci ta Mohammed Goni na daga cikin kokarin da ake na rage wahalhalun da tsadar rayuwa da ake fuskanta sakamakon janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
- Mayakan Boko Haram 78 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
- Mu Muka Harbo Jirgin Sojojin Nijeriya – Kasurgumin Dan Bindiga
A watan Yuli ne Zulum ya kaddamar da rabon kayan wanda ya tanadi gidaje sama da 300,000 tare da mutane kusan shida a kowane gida don kai wa mabukata miliyan 1.8.
A karkashin tsarin, duk wani mazaunin Feezan da ya cancanta ya karbi kayan abinci domin rage wahalhalu sakamakon tashin farashin kayayyaki.
A sabon rabon da aka yi a Feezan ga gidaje 2,000 da suka kunshi magidanta maza 1,000 da kuma mata 1,000 kowannensu ya samu buhun shinkafa daya da buhun wake.
Domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a tsarin, gwamnatin jihar Borno ta saka kungiyoyin farar hula da su kasance cikin kwamitin raba kayan agaji.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Zulum wanda kwamishinan kula da kananan hukumomi da masarautu, Hon. Sugun Mai Mele, ya ce unguwanni 15 a cikin birnin Maiduguri za su ci gajiyar inda kowace shiyya za ta karbi buhun shinkafa 2,000 da buhun wake 2,000.