Ingila ta samu damar buga wasan karshe na gasar kofin Duniya ta mata da ake bugawa a kasar Australia da New Zealand bayan fitar da masu masaukin baki.
A wasan da suka buga a filin wasa na Accor Stadium dake Australia kasar Ingila ta doke Masu masaukin bakin da ci 1-3.
- Tsadar Rayuwa: Gwamna Zulum Ya Raba Wa Magidanta 2000 Kayan Abinci
- Kwallon Mata: Abin Da Ya Kamata Ku Sani A Kan Wasan Ingila Da Australia
Shahararriyar yar kwallon Chelsea Samantha Keirr itace ta farke wa kasar ta kwallon da aka jefa mata a minti na 63.
Talla
Kafin Alessi Russo ta jefa ma Ingila kwallo ta uku kuma ta karshe a wasan da ya basu damar zuwa mataki na gaba.
Inda zasu hadu da kasar Sifen a wasan karshe na gasar kofin Duniya ta mata.
Talla