A zaman da kungiyar ‘yan kwadago ta yi da gwamnatin tarayya kan samun sauki game da hauhawar farashin kayayyakin more rayuwa wanda tsadar farashin man fetur ya haifar, an ta shi ba tare da wata kyakkyawar matsaya ba.
Taron an gudanar da shi ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayya da ke Abuja a yau Alhamis tsakanin gamayyar kungiyar ‘yan kwadago, NLC da ta ‘yan kasuwa, TUC kan tsadar rayuwa da ake ciki a fadin Nijeriya.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ƙarshen taron cewa, taron alama ce da ke nuna yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen tattaunawa da ‘yan ƙwadago a kan neman mafita game da halin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp