Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabi’u Kwankwaso, ya ce, duba da abubuwan da ke faruwa a Nijeriya a yanzun, ‘yan Nijeriya za su kada kuri’ar kawo sauyi na gaske a zaben 2027.
Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake karbar ‘ya’yan jam’iyyar APC fiye da 2,000 da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Kano.
- Gwamna Sani Zai Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Cutar Kansa Mai Gadaje 300 A Kaduna – Kwamishina
- Zargin Satar Biliyan 27: Tsohon Gwamnan Taraba, Ya Samu Beli
Kwankwaso wanda ya tarbi wadanda suka sauya shekar daga kananan hukumomin Dala, Kiru da Gwale na jihar a gidansa da ke Miller Road a Kano, ya ce, an “gasa wa ‘yan Nijeriya aya a hannu sosai”, don haka, babu abinda ya dace da su, face, shiga inuwar neman sauyi a 2027.
Ya bayyana sauya shekar ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa NNPP a matsayin wani abu mai tarihi, inda ya ce, adadin wadanda suka koma jam’iyyar NNPP daga unguwanni daban-daban na kananan hukumomin Dala, Kiru, Gwale da Dawakin Tofa na jihar, ya nuna cewa, tsarin APC ya ruguje gaba daya a yankunan.