‘Yan’uwana Zamfarawa da al’ummar Arewa da sauran ‘yan Nijeriya baki-daya, babu shakka; duk mai bibiyar al’amuran da ke tafiya a kasar nan, musamman wadanda suka shafi al’amuran siyasa da matsalar tsaro a yankinmu na Arewa; musamman kuma a Jihar Zamfara, zai tabbatar da irin dauki-ba-dadi da cece-kuce da zazzafar adawa da muhawarar siyasa da rashin shiri da kuma jituwar da ke gudana a tsakanin yaran mai girma Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle da kuma na mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare.
Allah ya sani, kuma shi ne shaida; domin kuwa za mu mutu mu kuma hadu a gabansa, ya yi mana hisabi.
- Sin Za Ta Zurfafa Hadin Gwiwa Da Bangarori Daban Daban Kan Shirin Ci Gaban Duniya
- Tallafin Daular Larabawa Ya Iso Nijeriya Ga Masu Ambaliya
Babu irin yunkuri da ba mu yi ba, domin ganin an samu daidaito da sasanci tare da fahimtar juna a tsakanin wadannan bangarori biyu, don a samu zaman lafiya, amma abin ya ci tura.
Sanin irin alhairin da ke tattare da samar da wannan hadin kai a tsakanin Ministan tsaron da kuma Gwamnan Jihar game da sha’anin matsalar tsaron da yake damun jihar tamu, yasa muka yi ta faman wannan yunkuri.
Kasancewar jihar ta Zamfara, na cikin jihohin da ke gaba-gaba wurin fuskantar matsalar tsaro a Nijeriya, shi yasa muke da ra’ayin cewa, lallai da za a samu cikakken hadin kai da fahimtar juna a tsakanin wadannan shugabanni namu guda biyu, ko shakka babu za a fi samun cikakkiyar nasara game da yakar ta’addanci da ‘yan ta’addar da suka addabi wnnan jiha.
Tun da dai tura ta kai bango, yau zan yi bayani na gaskiya kuma tsakanina da Allah, don haka duk mai suka; ba zan hana shi yi ba, haka nan mai yin zagi; shi ma ba zan hana shi yin zaginsa ba.
Gaskiya tsakanina da Allah, game da wannan rikice-rikicen siyasa da rashin jituwa da kuma rashin samun hadin kai a wannan jiha tamu ta Zamfara a tsakanin wadannan jagorori namu guda biyu, wato Gwamna Dauda da Minista Matawalle; duk wanda zai tsaya da kyau, ya yi adalci zai fahimci cewa; Bello Matawalle, ya fi karkata da amincewa a samu shiri da hadin kai da kuma fahimtar juna tsakaninsa da Gwamna Dauda.
Matawalle ya amince a zauna, a hada kai a yi aiki tare; domin fuskantar jihar ta Zamfara, amma duk da wannan; babu abin da ake kokarin yi, sai watsa masa kasa a fuska da tozarta shi da kuma kokarin cin dunduniyarsa tare da lullube duk wani kokari da yake yi na ganin an cimma nasara.
Babu shakka, mun bibiyi dukkanin su biyun, mun kuma nemi jin ta bakinsu tare da kokarin hada wasu manyan ‘yan siyasar jihar, kan don Allah a yi hakuri, a manta da duk abin da ya faru, a tsaya a fuskanci wannan matsala ta tsaro da talauci da ke addabar jiharmu. Amma tsakanina da Allah, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi kadai, mun samu cikakken hadin kai da goyon baya dari bisa dari daga bangaren Matawalle, amma ban da bangaren Gwamna Dauda, ko kadan ba mu samu goyon baya ba.
Kai hasali ma, mutanen Gwamna Dauda, har kullum idan kun nemi ganinsa, sai su yi banza da ku, suna tsammanin kamar wani abu kuke nema a wurinsa, ko kuma zuwa za ku yi domin yi masa fadanci ko banbadanci.
Don haka, ya kamata mutanen Gwamna Dauda; su bincika su ji, ba yabon kai ba; ba kuma alfahari ba, amma wallahi mu ba ma cikin masu bin ‘yan siyasa suna yi musu banbadanci da fadanci.
Tun da aka kirkiri Jihar Zamfara, Gwamnanta na farko Jibril Bala Yakubu, muna Zamfara ya hau mulki har ya gama, har zuwa Gwamna na biyu, Ahmad Sani Yariman Bakura; zuwa ga Mamuda Aliyu Shinkafi, zuwa ga Abdul’aziz Yari Abubakar; zuwa ga Muhammad Bello Matawalle, har zuwa ga shi kansa Gwamna Dauda da yake kan mulki a yau, idan akwai wanda muka nemi mu gan shi ko kuma muka nemi wani abu a wurinsa ko muka yi masa wani banbadanci ko fadanci, don Allah ya fito ya fada.
Allah ya sani, mu ci gaban jiharmu da zaman lafiyarta ne babban al’amarin da yake gabanmu. Sannan kuma, muna da yakini tare da tabbacin cewa, hadin kan Gwamna Dauda Lawal, a matsayinsa na shugaban tsaro a jiharsa (Chief Security Officer), da Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, zai taimaki al’ummar Jihar Zamfara baki-daya.
Har ila yau, hadin kansu da sasancinsu; wallahi zai taimaka wajen bayar da cikakkiyar natija da izinin Allah, wurin kawo karshen wannan bala’i na rashin tsaro da ke addabar wannan jiha tamu.
Amma tsakanina da Allah, ina mai yi muku rantsuwa da Allah; mun samu cikakken hadin kai daga bangaren Bello Matawalle, amma ba mu samu daga bangaren Gwamna Dauda ba.
Kamar yadda kuka sani, ni ba dan siyasa ba ne; amma wallahi ina da wani abu guda, wanda shi ne; da zarar Allah ya fahimtar da ni gaskiya, to fa zan goyi bayanta; na kuma karfafe ta ba tare da kallo ko la’akari da duk abin da mutane za su fada ba.
Allah shi ne shaida, tun muna magana da mutanen Matawalle, har ta kai ga muna magana da shi kansa Matawallen kai tsaye, ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba; ya yi mana rantsuwa da Allah tare da tabbatar mana da cewa, a shirye yake wajen bayar da dukkanin wani goyon bayan da ake bukata, domin samun tsaro a Arewa da kuma Jihar Zamfara baki-daya.
Haka zalika, Matawalle ya saurare mu; yana kuma ci gaba da sauraron mu a koda-yaushe. Sannan, ba wani abu yake ba mu ba, ba kuma ma neman komai a wurinsa; amma wallahi ya kira mu, mun kira shi; mun tattauna matsaloli tare, ya kuma nuna cewa al’ummarsa ce a gabansa, kuma shi mai sauraron al’ummar ne.
Amma daga bangaren Dauda Lawal, babu wani hadin kai ko goyon baya da muka samu. Hasali ma, babu wanda zai saurare ku; sannan ba su yarda da kowa ba tare kuma da tunanin cewa, kowa makwadaici ne da ke neman wani abu daga wurinsu.
Don haka, ya kamata su sani cewa; a da can ma ba mu nemi komai a hannun wani dan siyasar Jihar Zamfara ba, ballantana yanzu mu nema a hannun Gwamna Dauda. Kawai dai mu a matsayinmu na ‘ya’yan jihar ne, masu kishinta; shi yasa muke ta kokari tare da yunkurin ganin manyanmu sun ji tsoron Allah, sun hada kai; domin fuskantar wadannan dimbin fitintinu da suke addabar mu.
Ba ma fadanci, ba ma banbadanci, ba ma neman komai a wurin kowa sai Allah Subhanahu wa Ta’ala, mai bai wa kowa da kowa.
Kuma ya kamata mu sani, su wadancan munafukai, masu cin abinci da rigimar siyasar da ke tsakanin Matawalle da Dauda, duk abin da suke yi; Allah yana kallon su.
Haka zalik, masu kokarin kange Gwamna Dauda daga jama’a, wadanda ba sa so ya yi sulhu da Matawalle, suke zugawa tare da ruruta wutar fada a tsakaninsu; wallahi sai sun ji kunya da ikon Allah, domin kuwa sai jiharmu ta ci gaba; ta hanyar samun zaman lafiya.
Har ila yau, muna kira ga shi Gwamna Dauda; da ya ji tsoron Allah, ya kuma sani cewa; ina rantsuwa da Allah, mai kowa mai komai, a irin binciken kwakkwafi da sauraro da muka yi; mun fahimci cewa, Matawalle ba ya gaba da shi, bai kuma dauke shi a matsayin mikiyi ba kamar yadda ake ta kokarin nuna masa a koda-yaushe.
Kazalika, Matawalle ya yi mana rantsuwa da Allah da Alkur’ani cewa; al’umma ce a gabansa, ba gaba da Dauda ko kiyayya ba. Don haka, a shirye yake ku hada kai; ku yi aiki tare, domin magance wannan matsala da ta addabi Jihar Zamfara.
Ba mu ce dole sai kun yi siyasa ko jam’iyya daya ba, manufarmu ita ce; kowa ya yi siyasarsa, amma ku hada kai domin ci gaban jiharmu. Mu sani, mulki na Allah ne; yana iya bayar da shi ga duk wanda ya so, yana kuma iya kwace shi ga duk wanda ya so.
Allah ya kaddara Bello Matawalle ya zama Ministan Tsaro, kai kuma ya kaddara ka zama Gwamnan Jiha, don haka me ya kamata ku yi? Sai ku hada kai, domin ceto jihar tare da kawo mata dukkannin wani ci gaban da ya dace.
Babu shakka, na sani cewa; Gwamna Dauda, wannan rubutu ba zai yi maka dadi ba; kai da magoya bayanka, amma ina kira da ku yi hakuri, wannan ita ce tsantsar gaskiya mai daci; wadda ban yi tsammanin na kusa da kai za su iya fada maka ba cewa, wannan matsala ta rashin jituwa tsakaninka da Matawalle daga bangarenka matsalar take.
Muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala, ya sa ku gane hakan; ku kuma gyara, amin.
Daga karshe, muna addu’a da rokon Allah SWT, ya kawo mana zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jiharmu ta Zamfara da sauran yankunanmu na Arewa da ma Nijeriya baki-daya.