Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da kayan shan ruwan wanda samari ke kaiwa ‘yan matansu wato Ramadan Basket.
- INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi
- Masanin Tattalin Arziki: Kasar Sin Ce Karfin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
A kowacce shekara matasa maza na kokarin zage dantse wajen ganin sun nuna bajintarsu ga ‘yan matansu, musamman wajen yi musu kayan shan ruwa (Ramadan Basket) na gani na fada.
Sai dai kuma rashin yin hakan ko karancin kayan na janyo ka ce-na ce gami da samun sabani tsakanin masoyan.
Yayin da a gefe guda kuma ake samun samari masu kokarin zamewa a soyayyar har sai bayan sallah. Sai dai kuma abun mamakin daya faru cikin wannan watan na Ramadana a wasu guraren shi ne; Madadin samari su kaiwa ‘yan matansu Ramadan Basket, Mata ne ke kaiwa samarinsu.
Ko Mata za su iya jure yi wa samari Ramadan Basket idan har aka ce Ramadan Basket ya tashi daga kan Maza ya koma kan Mata, matsayin su ne wadanda za su rinka yi wa samarin a kowacce shekara?, Matsayinki na ‘ya mace ko za ki iya iy wa saurayinki Ramadan Basket?, haka kai ma matsayinka na namiji idan budurwarka ta kaho maka Ramadan Basket za ka iya karba?, Nawa za ki iya kashewa saurayinki wajen yi masa Ramadan Basket, musamman yadda Mazan ke kokarin kashe nasu kudaden wasu ma har su ciwo bashi?, ko ya matasa ke daukar Ramadan Basket a wajensu?. Mabiya shafin Taskira sun bayyana na su ra’ayoyin kamar haka:
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi daga Jihar Kano:
A gaskiya Ramadan Basket ace in yi wa saurayi da matsala, bana tunanin zan iya yi mishi, yawancin masu yi wa ‘yan mata Ramadan Basket in ka duba samari ne ba masu aure bane, saboda kila wani yana da mata biyu ko uku ta Ina zai yi miki wani wai Ramadan Basket?, a gaskiya samari su daina damun kansu wajen tilastawa kansu yin Ramadan basket Allah ya sa mu dace.
Sunana Musbahu Muhammad Goron Dutse daga Jihar Kano:
Idan budurwata ta kawo min wallahi karba zan yi har da godiya. Wannan amsar sai mata. Al’ada ne da kuma kyautatawa a tsakanin masoya. Ya kamata a rage buri da karya, samari su yi abu daidai karfinsu ‘yan mata su karbi abin da ya samu su saka albarka.
Sunana Nura Ibrahim (Been Noor Ne), daga Jihar Katsina Karamar hukumar Malumfashi:
Eh daman ai ya kamata tunda abin rage radadi ne, musamman ma dai yanzu da maza ke wahala kafin su samu kudi ga rana in ta bashi ba ta yi laifi ba, face jarumta. Eh! kwarai kuwa zan karba nayi godiya, kuma nayi addu’ar Allah ya kara budi na alkhairi. Daman mai kyautata maka ka kyautata mashi, Na dauki Ramadan Basket Kamar kyautatawa ce da kuma rage radadi. Ina mai bawa ‘yan uwa na samari da su ci gaba da kyautatawa ‘yan matansu, amma idan suna da hali kada ganin wani yayi, ka ce kai ma sai kayi, hakan zai haifar da damuwa.
Sunana Khaleep Saleh Tabla daga Jihar Bauchi:
Kamar kin san abin da yake tafiya a zamin yanzu kenan, saboda ni ma farkon azumin nan haka ta kawo min Ramadan Basket. Na dauke shi, kyautatawa tsakanin masoya irin wadda ake ware mata lokaci na musamman ake mikata dan nuna kulawa ga masoyiya. Shawarata ga samari da su ‘yan matan a rage buri, domin abu ne na nishadi na kulawa da nuna so da kauna ga masoya, bai kamata kuma a rinka zurfafa buri yayi yawa ba har ta kai ga marashi yana jin kunyar zuwa wajen budursa, in kana da hali kayi, in ba ka da shi ka kyale.
Sunana Safiyya Mustapha Mu’az daga Gurin Gawa:
A’a! ba zan iya ba, kawai dai idan zai zo gidanmu zan hada mishi kayan shan ruwa dai-dai karfina. To a gaskiya Idan ni ce, zan kashe mishi iya kar abin da Allah ya hore min, babzan takura kaina ba ko iyayena ba wurin ganin na yi masa gwaninta ba, wacce ta zamanto zamanto zan hada da karya ba, zan bashi abin da Allah ya hore min idan ya ga zai iya ci gaba da soyayya da ni shikenan, Idan kuma ya raina abin da nayi mishi a matsayina na ‘ya mace zai iya canza wata budurwar, wadda za ta hada mishi da yawa. To ni dai inda na dauki Ramadan Basket kyauta ce wacce samari ke bawa ‘yan matansu a cikin watan Ramadan, wanda ake kira da Ramadan Basket, haka ma ‘yan mata kan bawa samarin da suke so dan kyautatawa junansu wannan ba laifi bane idan har suna da damar da za su bayar da kyautar ga junansu. Shawarata anan ita ce ga matasa da kuma ‘yan mata ka da su takurawa kansu akan abun da bai zama lallai ba, idan ka samu ka bayar, idan kuma baka samu ba ka hakura, kada ka takurawa kanka kawai ka bata kyautar dadadan kalaman soyayya, wanda zai mantar da ita cewa baka bata Ramadan Basket ba. Saboda wata budurwar ta fi son wannan kalaman fiye da kayayyakin da za ka bata, haka ke ma budurwa idan saurayinki bai samu damar baki ba dan Allah ki kwantar da hankalinki ki fahimce shi ki yi mishi uziri ka da akan bai baki Ramadan Basket ba ki canza mishi fuska ki daina sauraransa, ki daina bashi kulawar da kike bashi a baya, Hmm ki nuna mishi cewa ke fa shi din kike so ba wai kayansa ba, kuma kulawarsa kike so ba wai abin hannunsa ba hakan zai kara sawa ku fahimci junanku, soyayyarku kuma ta zamo abar kwatance.
Sunana Ibraheem Isama’il Ibraheem daga Jihar Kano:
Gaskiya zan karba sabida kar ka zama mai mayar da hannun kyauta baya, kamar kyautatawa ce ita kuma kyautatawa tana kara dankon soyayya. Ni kam abin da na dauke shi shi ne; mutunta juna ne da kuma kyautatawa juna a soyayya. Shawarata ita ce abu ne mai kyau duk da ba dole bane, amma kar mace ta dauka idan lokacin ya zo dan namji bai yi mata ba kamar baya sonta ne, ta dauka ko ba wannan lokacin da ma mai hidimta mata ne, kuma idan yana dashi zai yi. Allah ya sa mu dace, Allah ya bada yadda kowa zai fita kunya walau mace ko namiji.
Sunana Yakubu Obida daga Farawa Jihar Kano:
Zan iya yi wa budurwata kayan shan ruwa ma’ana Ramadan Basket. Ramadan basket ba komai bane illa hanya ta kyautatawa, da kuma taimakon juna, domin a samu sauki wajen yin ibada a sami na bude baki da kuma sahur. Gaskiya bai kamata mutum ya sa rai akan za a yi masa Ramadan Basket ba, saboda yanayi na rayuwa dan an yi miki wannan shekarar bai zama lalle wata shekarar ayi miki ba, don babu tabbas, saboda yau da gobe.
Sunana Shafaatu Muhd Tukur daga Jihar Kano Unguwar Gama, Karamar hukumar Nassarawa:
Idan ni ce zan kashe kudade masu yawa kamar dubu talatin ko fiye da haka don jin dadin wanda nake so. Ina daukar Ramadan Basket da mahimmanci, saboda yana nuna cewa saurayina yana sona kuma yana so ya sanya ni cikin farinci don futar dani kunyar kawayena. Abun da zan bada shawara shi ne; duk abin da zamu yi mu yi shi daidai gwargwado don gudu fadawa.