Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya shelanta cewa, rashin wanzar da tsarin ba aiki ba biyan Albashi ne ya jinkirta yin sulhu a tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar malaman Jami’oin kasar nan (ASUU).
Adamu ya sanar da hakan ne ayau Alhamis a taron manema labarai karo na 47 a fadar shugaban kasa da tawagar sadarwa ta shirya.
Ya bayyana cewa, ASUU taki janye wa daga yajin aikin da take yi saboda bukatar ta na cewa, sai an biya malaman daukacin Albashin da suke bi a lokacin da suke yin yajin aikin, bukatar da kuma Gwamnatin Tarayya taki amince wa da ita.
Adamu ya ci gaba da cewa, sai dai kungiyoyi hudu ba Jami’oin dake a fadin kasar nan daga cikin biyar, sun amince za su janye daga yajin aikin a tsakanin sati daya, inda ya sanar da cewa, wannan matsayar za a iya kawai sanar wa ne bayan an tattauna da shugabannin su.
Da yake yin tsokaci a kan biyan daliban Jami’oin diyya kan lokacin da suka bata saboda yajin aikin kungiyar har na tsawon wata shida, Adamu ya ce, wannan nauyi ne da ke a kan ASUU amma ba a kan Gwamnatin Tarayya ba.