Ya ku ‘yan’uwana ‘yan Nijeriya, ya ku ‘yan’uwana ‘yan Arewa! Kamar yadda kuka sani kuma kuke jin labari cewa, wasu ‘Yan Majalisun Tarayyar Nijeriya 60 zuwa 90, wadanda suka sa wa kansu suna: ‘Parliamentary Group’, karkashin jagorancin dan majalisa daga Jihar Legas, Mista Wale Raji.
Tuni dai wadannan ‘yan majalisa suka fara gwagwarmayar gabatar da bukatar cewa, tilas dole sai kasar nan ta yi watsi da tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken iko (Federal System), wanda a yanzu haka ake amfani da shi a wannan kasa da muke ciki, domin komawa tsarin mulkin Firaminista ko Faliyamentari (Parliamentary System) kamar yadda aka yi a Jamhuriya ta farko, wai don a karkatar da kudaden da ake kashewa; domin yi wa talakawan kasa aiki.
- Babban Jami’in JKS Ya Bukaci A Himmantu Wajen Ciyar Da Kokarin Dunkulewar Kasar Gaba
- Zaben Fitar Da Gwani Na APC A Edo Ya Bar Baya Da Kura
Tabbas wannan zance ga duk mai sauraro zai ji cewa, akwai alamun kanshin gaskiya a cikinsa, amma abin tambayar shi ne; anya babu wata makarkashiya a karkashinsa?
Dan majalisa daga Jihar Ribas, shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, shi ne ya dauki nauyin gabatar da kudirin har guda uku, duk dai a kan wannan bukata.
Wadannan ‘yan majalisu sun bayyana cewa, ganin yadda ake kashe makudan kudade ba tare da kakkautawa ba, musamman wajen tafiyar da tsarin shugaban kasar da ake amfani da shi a halin yanzu, wanda yake lakume dimbin biliyoyin Naira, wadanda ya dace a yi wa talakawa aiki da su; wajen harkar bayar da ilimi da kula da lafiya da kuma yadda ake hana kasa ci gaba tare kuma da magance irin karfin fada a jin da bangaren zartawa, wato bangaren shugaban kasa ya ke da shi da kuma wadanda ya ke nadawa a mukamai daban-daban, duk ya dace a sake nazari a kansu; domin sama wa wannan kasa mafita.
Wannan aiki kamar yadda muka sani, ko shakka babu za su yi shi ne ta hanyar yin gyara ga kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, domin samun saukin kai wa ga manufofinsu na barin wannan tsari na shugaba mai cikakken iko zuwa ga tsarin Firaminista.
Har ila yau, shugaban wannan tafiya baki-daya kamar yadda na ambata shi ne, Mista Wale Raji, dan majalisa mai wakiltar Jihar Legas daga jam’iyya mai mulki ta APC.
Mai magana da yawun wadannan ‘yan majalisa ta wakilai su kimanin 60 da suka gabatar da bukatar a cikin shirin yi wa kundin tsarin mulkin garambawul, wato Hon. Abdulsamad Dasuki, mai wakiltar Kebbe da Tambuwal daga Jihar Sakkwato cewa ya yi, suna matukar damuwa da irin makudan kudaden da ke tafiya a bangaren zartarwa da kuma karfin fada a ji, wanda tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken iko ya ke da shi a karkashin wannan tsari.
Dasuki ya kara da cewa, a baya duk kokarin da majalisun tarayya suka yi wajen rage kudaden da ake kashewa a bangaren shugaban kasar da kuma rage wa shugaban karfin fada a ji, ya ci tura saboda masu cin gajiyar tsarin, domin kuwa su ma ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kawo wa wannan yunkuri cikas.
“Duk da cewa wannan gyara ne da zai dauki tsawon lokaci tare da bukatar fadakar da jama’ar kasa, don goyon bayan tsarin; suna da yakinin cewa, ko da ba a samu biyan bukata a karkashin wannan majalisa ba, to kuwa ana iya samu a karkashin majalisar da za ta biyo bayanta”, in ji shi.
‘Yan’uwana masu girma, tabbas kamar dai yadda muka sani, a karkashin tsarin mulkin Firaminista da aka yi amfani da shi a Jamhuriya ta farko, bangaren zartarwa na samun karfi ne daga bangaren majalisar dokoki, inda ake zabo firaminista da kuma ministocinsa daga majalisar, matakin da ya ke takaita kashe makudan kudade a bangaren fadar shugaban kasa da kuma ministocinsa.
Sannan wannan yunkuri da tsarin da ake so a kawo, mafi yawan ‘yan Nijeriya da kuma da dama daga cikin al’ummar yankin Arewa, suna kallon sa a matsayin wanda shugaban kasa ne ke yunkurin kawowa tare da goyawa baya, amma wanda majalisar ke bukatar aiwatarwa bayan kammala wa’adi biyu na shekara 8 na shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2031, ana kuma yi ne tare da hadin bakinsa shugaban kasar.
Babu shakka an bayyana cewa, shugaban kasar da wasu mutane daga yankin kudu, na da hannu dumu-dumu a cikin wannan tsari, duk da cewa kuma tsarin ba zai tabbata yanzu ba; har sai shugaban kasar ya kammala wa’adin shekarunsa takwas, sannan a aiwatar da shi a shekarar 2031.
Wannan dalili ne yasa muke kira da cewa, ya zama wajibi a yi taka-tsan-tsan, domin idan ba haka ba; me ya sa sai shekarar 2031? Me ya sa ba za a yi yanzu ba, har sai Tinubu ya gama nasa mulkin?
Da ma can, da yawa daga cikin ‘yan Arewa na da shakku gami da zargi game da irin yadda shugaban kasar ke ta kwashe wasu muhimman bangarori na wasu manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya zuwa Jihar Legas.
Domin kuwa, an dauke wasu sassa na babban bankin kasa (CBN), da wasu daga ma’aikatar hukumar jiragen sama (FAAN), da kuma wasu daga bangarorin ma’aikatar mai ta kasa (NNPC); da wasu muhimman wurare na gwamnatin tarayya, duk aka mayar da su Legas; kai hatta ma makarantar horar da manyan hafsoshin soja da ke kasar nan (NDA), da ke Jihar Kaduna, wallahi na samu gamsasshen labari cewa, za a mayar da wasu muhimman wurare daga cikinta zuwa Legas.
Hakan na nuna cewa, babu yadda za a yi duk wani hafsan soja ya kammala karatunsa a Kaduna, ba tare da ya dangana zuwa Legas ba, a can ne zai kammala karatun nasa; ba a Kaduna kamar yadda aka saba ba.
‘Yan’uwana masu girma, gaskiyar magana ita ce; duk irin wadannan abubuwa da suke faruwa, dole ne su jawo zarge-zarge da cece-kuce tare da rashin yarda a tsakanin wannan gwamnati da al’ummar yankin Arewacin Nijeriya.
Sannan bayan wannan, yana daga cikin dalilan da suka sa muka ce ya kamata mu yi taka-tsan-tsan da wannan al’amari, kar mu yadda mu bari a yi amfani da wasu daga cikin ‘yan’uwanmu ‘yan majalisa, a cusa wani tsari wanda zai cutar da yankinmu na Arewa, sannan mun ji kishin-kishin cewa, wai idan har aka dawo kan wancan tsari, dole ne a cire wasu jihohi daga cikin yankin Arewar. Ko kuma a cire yankin da ake kira da Midil Belt (Middle-Belt) ko Arewa ta tsakiya (North Central), kuma wannan ba don komai ba, sai don a kassara Arewar ko kuma a rage mata karfi ko yawa.
A cewar zargin, wai ba za a yarda a koma wancan tsarin da aka yi a baya ba na yankuna guda shida da suka hadu suka yi Nijeriya (SID GEOPOLITICAL ZONES) ba. Wadanda suka hada da yankin Arewa maso yamma (North West Region) da yankin Arewa maso gabas (North East Region) da yankin Arewa ta tsakiya (North Central Region) da yankin kudu maso yamma (South West Region) da yankin kudu maso gabas (South East Region) da kuma yankin kudu maso kudu (South-South Region).
Yankin Midil Belt da suke magana, ya hada Jihohin Arewa guda tara ne kamar haka: Jihohin Filato, Adamawa, Babban Birnin Tarayyar Najeriya (Abuja), Benuwe, Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa da kuma Taraba.
Don haka, ana so a yi amfani da banbancin addinin da ke tsakaninmu da na yare da kabilanci a cire su daga cikin yankin Arewa, domin a rage mana karfi. Saboda haka, ina kira ga ‘yan’uwana ‘yan Najeriya baki-daya, musamman ‘yan Arewa da cewa, ya zama wajibi mu yi hankali tare yin taka-tsan-tsan da wannan tsari, ka da mu yarda a yaudare mu.
Kamar yadda aka sani ne cewa, Sir Abubakar Tafawa Balewa shi ne Firaministan Nijeriya na farko, wanda ya karbi mulki daga hannun turawan mulkin mallaka a lokacin samun ‘yancin kai; Dakta Nnamdi Azikiwe kuma a matsayin shugaban kasa na jeka-na-yi-ka, kafin wasu miyagun sojoji, makiya Nijeriya su hambarar da gwamnatinsa tare da hallaka shi, yayin da suka sake dora kasar a karkashin tsarin gwamnati irin na Amurka, mai dauke da shugaban kasa mai cikakken iko.
Har ila yau, Kasar Nijeriya ta tafiyar da irin wannan tsarin mulki ne na Faliyamantari tun kafin samun ‘yancin kai har zuwa lokacin jamhuriya ta farko. Amma daga baya juyin mulkin 15 ga watan Janairun 1966, wanda sojoji suka yi ya kawo karshen jamhuriyyar ta farko.
Sojoji sun hambarar da wancan tsari na farar hula, suka mulki Nijeriya har zuwa lokacin da suka mika mulki hannun farar hular a shekarar 1979, amma sai suka gina jamhuriyya ta biyun a kan tsarin mulkin 1979, wanda shi ne farkon tafiyar da kasar a kan tsarin Federaliyyah, wanda aka dauko daga Kasar Amurka.
Haka zalika, rahotanni masu karfi sun bayyana cewa; wadannan ‘yan majalisa da suka rattaba hannu a kan wannan bukata, sun fito ne daga daukacin jam’iyyun da ke cikin majalisar daban-daban, ciki har da jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP, babbar jam’iyyar adawa.
Don haka, muna kiran su baki-daya da cewa wallahi su yi a hankali kuma su yi taka-tsan-tsan. Domin kuwa, wannan badakala ta tuna min da wani zance mai kama da karin magana, wanda ake dangantawa zuwa ga Khalifan Manzon Allah (SAW) na hudu, wato Aliyu Dan Abi Talib, Allah ya kara masa yarda; a lokacin da ya kalubalanci Khawarijawa a zamaninsa, a lokacin da suka so su yi amfani da wani zance na gaskiya, amma ba gaskiyar suke nufi ba; wato akwai wata manufa ta kawo tashin hankali da zubar da jinin bayin Allah a cikin zuciyarsu. Sai suka ce wa Aliyu Dan Abu Talib, Allah ya kara masa yarda: hukunci da mulki duk na Allah ne shi kadai, kun ga wannan zance nasu gaskiya ne, amma su ba gaskiyar ce manufarsu ba. Sai ya mayar musu da martani da wannan shahararriyar kalmar tasa cewa: “Wannan magana tasu gaskiya ce, amma su barna suka nufa da ita ba gaskiya ba.”
Saboda haka, bincike ya tabbatar da tsarin shugabanci irin na Firaminista; tsari ne mai kyau. Domin kuwa ko babu komai, talakawa za su iya amfana da gwamnati a cikin sauki. Da dama daga cikin wadanda ke kokawar neman kujerar zama gwamna, za su koma neman kujerar shugabancin karamar hukuma. Sannan, kananan hukumomi za su dawo suna amfanar da al’umma, kamar yadda ake yi a can baya. Wannan kadan ne daga cikin alfanun wannan tsari, yana kuma da saukin kashe kudi wajen tafiyar da mulki.
Allah ya sa mu dace, ya taimake mu, ya zaunar da kasarmu lafiya, ya kawo mana wadatar arziki ya kuma magance mana dukkanin matsalolin kasarmu Nijeriya baki-daya, amin.
Na gode,
Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a wannan lamba kamar haka: 08038289761.