Manazarta ayyukan sama jannati sun bayyana cewa, tsarin tantance ayyukan likitanci na sararin samaniya, zai ingiza nasarar binciken samaniya yadda ya kamata.
Yayin taron dandali na biyu game da binciken tsarin ayyukan likitanci na sararin samaniya na kasar Sin da aka bude a Asabar din nan a birnin Hangzhou, na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, mahalarta taron sun ce cibiyar binciken samaniya ta Sin ta cimma nasarori a fannin tsarin ayyukan likitanci na sararin samaniya, wanda hakan zai ingiza nasarar shirin sauka a duniyar wata, da sauran ayyuka masu nasaba da aikin sama jannati.
- Xi Ya Jaddada Samar Da Karin Kwararrun Jami’ai Ga Xinjiang
- Fasahar Sin Ta Kara Habaka Sha’anin Zirga-zirgar Ababen Hawa Mara Gurbata Muhalli A Afrika
Yayin taron na yini biyu, kwararru da masana za su yi musaya kan nazari, da ayyukan ci gaba da aka lalubo a fannin tsarin ayyukan likitanci na sararin samaniya, kana za a tattauna kan muhimman batutuwa, kamar yiwuwar dan Adam ya rayu a yankunan samaniya masu nisa yayin ayyukan sama jannati.
Da yake tsokaci game da hakan yayin bude taron, mataimakin shugaban tsare tsaren ayyukan sama jannati na kasar Sin, kana dan sama jannati na farko a kasar Sin Yang Liwei, ya ce tallafin samar da kwarewa a fannonin ayyukan likitanci na sararin samaniya, muhimmin bangare ne na wanzar da ci gaban ayyukan bunkasa bincike, a cibiyar binciken samaniya ta kasar Sin, da tsarin aiwatar da shirin binciken duniyar wata na ‘yan sama jannati, wanda dukkaninsu suka haifar da sabbin damammaki a fannin bunkasa tsarin ayyukan likitanci na sararin samaniya.
Bugu da kari, tsarin ayyukan likitanci na sararin samaniya na taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar kiwon lafiyar al’umma. Tare da samar da tallafi, da dandalin gudanar da bincike kan sassan kula da lafiyar zuciya, da sassan tsoka da kashin ‘yan sama jannati, da batun tsufan jikin dan adam, da samar da kariya ga magunguna, da tantance ingancin su. (Mai fassara: Saminu Alhassan)