Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan kafa Ma’aikatar Raya Albarkatun Kiwon Dabbobi, ya ce hakan wani muhimmin tsari ne na amfani da damar da ke cikin ɓangaren kiwo da kuma inganta sarrafa kayayyakin da ake samarwa.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da yake jawabi a Taron Shekara-shekara na Hukumar Gidajen Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN) da aka gudanar a Abuja, mai taken “Samar da Abinci a Nijeriya: Ina Mafita?”
- Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Legas Za Ta Kara Samar Da Kwararru – Kwamishina
- Mutum 10 Sun Mutu A Turmutsutsin Rabon Shinkafa A Abuja
Ya ce: “Ba a jima ba da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), ya ɗauki wani gagarumin mataki na kafa Ma’aikatar Raya Albarkatun Kiwon Dabbobi. Wannan tsari mai muhimmanci ya nuna yadda gwamnatin ta fahimci irin damar da ke cikin harkar kiwon dabbobi, wanda ake kira tushen da ba a yi amfani da shi ba.”
Ministan ya jaddada cewa tabbatar da wadatar abinci yana da matuƙar muhimmanci ga tsaron ƙasa, zaman lafiya, da cin gashin kai.
Wannan ne ya sa Shugaba Tinubu ya sake fasalin sunan Ma’aikatar Noma da Raya Yankunan Karkara zuwa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci.
Ya ce: “Nijeriya, wadda Allah ya albarkace ta da ƙasa mai yalwa, yanayi mai kyau, da matasa da ke cike da kuzari, tana da damar zama jagorar noma a duniya. Amma har yanzu muna fama da ƙalubale wajen samar da abinci mai arha kuma wadatacce.
“Wannan ƙalubale ne da ya sa Shugaban Ƙasa ya mai da hankali sosai ga wannan muhimmin ɓangare, wanda shi ne babbar hanyar samar da ayyukan yi a ƙasar nan.”
Idris ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakai masu muhimmanci, ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci kan samar da abinci, ƙaddamar da shirin samar da abinci mai ɗorewa, da kuma yaƙi da masu ɓoye kaya da masu fasa-ƙwauri, domin tabbatar da samun kayan abinci cikin sauƙi da arha.
“Babu abin da ba za a iya cimmawa ba wajen samar da abinci a Nijeriya, musamman idan muka haɗa kai; za mu iya canza ƙasar mu zuwa ƙasar da take da yalwar abinci, inda babu wani ɗan Nijeriya da zai kwanta da yunwa.
“Na tabbata cewa babban baƙo mai gabatar da jawabi da sauran ƙwararru za su yi cikakken bayani kan ƙalubalen da harkar noma ke fuskanta tare da bayar da hanyoyin magance su,” inji shi.
Ministan ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su taka muhimmiyar rawa wajen inganta samar da abinci ta hanyar ilimantar da manoma kan dabarun zamani, canjin yanayi, da kuma tallafin da gwamnati ke bayarwa domin ƙara yawan amfanin gona.
Idris ya yaba wa FRCN bisa farfaɗo da wannan Taron Shekara-shekara ɗin, inda ya yaba da ƙudirin ta na bunƙasa cigaban ƙasa ta hanyar shirye-shirye da kuma tsare-tsare masu tasiri.
Taron ya samu halartar manyan baƙi kamar Ministan Raya Albarkatun Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Muktar; Ƙaramin Ministan Noma da Tabbatar da Wadatar Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi; Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli; da Sarkin Wase a Jihar Filato, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna.