A yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada cewa, tsarin zamanantar da kasar Sin, tsari ne na ci gaba da kare hakkin dan Adam, kuma kasar Sin za ta kara himma wajen ba da dama ga dukkan jama’a wajen more daidaiton ‘yanci na tattalin arziki, zamantakewa da al’adu a matsayi mafi girma.
Wang ya kuma bayyana yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa kan wannan batu cewa, a kwanakin baya ne kwamitin MDD mai kula da harkokin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu ya gudanar da nazari a birnin Geneva na kasar Switzerland, kan yadda kasar Sin ta aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasa kan ‘yancin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu.(Ibrahim)