Sakataren jam’iyyar APC, Dakta Raymond Chidama, ya musanta batun dakatar da ‘yar takaran kujerar gwamnan jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani daga jam’iyyar.
Sakataren ya bayyana haka a zantawar da LEADERSHIP Hausa ta yi da shi ta waya a ranar Juma’a, inda ya ce shugabannin jam’iyya daga matakin unguwa ba su da hurumin korar wani mutum daga jam’iyya.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 7, Sun Kwato Makamai A Kaduna
- NEF Ga Buhari: Kar Ka Sake A Karkashin Mulkinka Ka Bari IPOB Ta Hana ‘Yan NIjeriya Kada Kuri’a
“Doka ba ta ba da dama ga shugabannin jam’iyya daga matakin unguwa su kori wani a jam’iyya ba.
“Don haka babu wanda ya kori mai girma ‘yar takarar gwamnanmu, Sanata Aishatu Ahmad Binani daga jam’iyya.
“Abin da aka yi laifi ne, kuma jam’iyya za ta kafa kwamitin bincike domin hukunta wadanda aka samu da laifin karya dokar jam’iyya” in ji Chidama.
Rahotanni daga mazabar Binani sun bayyana cewa mutum 21 daga shugabannin jam’iyyar sun sa hannu kan takardar dakatar da Sanata Binani daga jam’iyyar APC.