Idan Allah Ubangiji ya kai mu ranar 1 ga watan Agustan 2023, NIS, Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa za ta cika shekara 60 da kafuwa a matsayin hukumar gwamnati da aka ɗora wa alhakin kula da al’amuran shige da fice a cikin ƙasar nan, da bayar da izinin zama a cikin ƙasa ga baƙin ƙasashen waje, da bayar da takardun biza ga waɗanda ba ‘Yan Nijeriya ba da ke neman shigo ƙasar don gudanar da harkokin kasuwanci, zuba jari, yawon buɗe ido, ziyara, aikin gyara ko wata harka da ta shafi shige da ficen baƙi.
Hukumar tana gudanar da ayyuka da dama domin tabbatar da cewa bara-gurbin baƙi ba su shigo sun ɓata mana ƙasa ba. Wannan ya sa hukumar ta NIS ta tsara yadda za ta riƙa gudanar da ayyukan sintiri domin inganta tsaro a iyakokin Nijeriya na ruwa da kan-tudu, da kuma kare tattalin arzikin ƙasa daga masu zagon ƙasa walau a cikin ƙasa ko wajenta, da hana haramtattun baƙin-haure daga tsallakowa cikin ƙasa.
An samar da sintiri na musamman a kan iyakokin ƙasa ne domin ƙara ƙarfafa ƙoƙarin da jami’an hukumar ke yi a sansanonin kula da iyakoki ko shingen bincike domin rage faɗin wuraren da ba a iya kaiwa gare su a bakin iyakokin ƙasa.
Galibin ‘Yan Nijeriya kan yi ƙorafi a kan rashin tsaron iyakokin ƙasa amma kuma yawanci abubuwan da ake faɗa babu wasu ƙwararan hujjoji a kai ko bayanan ƙwararru da masana da ke tabbatar da sahihancin abubuwan da ake yamaɗiɗi a kai.
Domin akwai jami’ai da suke aikin sintiri ba dare ba rana tsawon sa’o’i 24 a kullu yaumin cikin ranakun mako domin tabbatar da tsaron iyakoki. Mun san cewa akwai wasu wurare da ba a iya kaiwa gare su saboda faɗin ƙasa da muke da shi wanda ta amfani da kimiyya da fasaha ne kawai za a iya kaiwa gare su. Su ma a halin yanzu an lalubo bakin ɗaren kaiwa gare su sakamakon gina katafariyar cibiyar fasahar sadarwa a shalkwatar NIS da ke Abuja.
A wannan katafariyar cibiyar, akwai sashen karɓar bayanai da bayar da umarni wanda ta nan ana iya saka ido a kan duk abubuwan da ke faruwa a manyan iyakokin shiga ƙasa. Ana nan ana kan gwaji a kan wannan sabuwar dabara da aka yi amannar tana haifar da ɗa mai ido.
Bugu da ƙari, hukumar ta samar da sansanonin jami’ai masu sintirin iyakokin ƙasa guda 30 a sassa daban-daban na ƙasar nan domin cike gurbin da ake da shi na kula da iyakoki.
NIS tana da ƙwararrun jami’ai masu jini a jika da ke aiki gaba-gaɗi wajen tabbatar da tsaron iyakokin ƙasa da kula da harkokin shige da fice domin kare Nijeriya daga bara-gurbin baƙi da kuma taimaka wa hanyoyin bunƙasa ci gaban ƙasar.
Hukumar ta samar da wani tsari da aka yi wa laƙabi da “Manufar Bizar Nijeriya ta 2020” da nufin magance duk wasu lamura da suka shafi biza da kuma cimma buƙatun haɓaka ingantaccen kasuwanci da samar da kyakkyawan yanayin saka hannun jari, da bunƙasa yawon shaƙatawa, shigowar baƙi da kuma haɓaka masana’antu da ɗaukaka ci gaban fasaha.
An raba sashen kula da harkokin shige da fice zuwa gida biyu, akwai ɓangaren kula da shige da ficen baƙi bisa ƙa’ida akwai kuma wanda yake kula da harkokin baƙin-haure da ke silalowa cikin ƙasa ba bisa doka ba.
Dukkansu suna aiki kafaɗa da kafaɗa wajen sanya ido domin hana baƙin-haure cin karensu babu babbaka da kuma tabbatar da sauƙaƙa harkokin shige da ficen baƙin da ke shigowa bisa ƙa’ida da doka, duk dai don ganin Nijeriya na cin gajiyar harkokin shige da fice yadda ya kamata a duniya.
Har ila yau, a ƙarƙashin waɗannan manyan ɓangarorin na kula da shige da fice, akwai sansanoni da aka kakkafa don kula da masu shiga ko fitar ƙasa a kan iyakoki. Ana samun waɗannan sansanoni a dab da iyakokin ƙasa. Sannan akwai sashen da yake kula da masu shigowa cikin ƙasa ta hanyar amfani da biza. Kana akwai sashen kula da sintiri da lura da abubuwan da ke kai-komo. Wannan shi ma ya kasu, akwai ɓangaren kula da iyakoki na kan-tudu, akwai na kula da iyakokin ruwa sannan akwai na kula da filayen jiragen sama. Dukkansu suna aiki ne kai-tsaye da sansanonin kula da iyakoki da kuma shingen bincike. Bugu da ƙari, ko bayan waɗannan, akwai wasu zaratan jami’ai da ke sa ido da kai ziyara a otel-otel da kamfanonin da suke aiki da baƙi ‘yan ƙasashen waje domin tabbatar da ba a rufe ƙofa da ɓarawo ba.
A bisa ƙa’ida, kowane kamfani da yake aikin kasuwanci a Nijeriya da halastaccen izinin kasuwanci a cikin ƙasa wajibi ne ya samu kason da ake warewa na ƙwararrun da ke aiki a ƙasa domin jin daɗin gudanar da aikinsa. Nijeriya tana da tsare-tsare na harkokin kasuwanci da zuba jari masu ƙayatarwa, shi ya sa ƙasar ta samar da tsarin biza hawa-hawa, akwai na rukuni na musamman guda uku da kuma rukuni mai matakai 79 domin biyan buƙatun masu nema daga ko ina a faɗin duniya.
A cikin shekara 60 da ta yi da kafuwa, Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar samar da fasfo mai ƙarko da ya zama irinsa na farko a Afirka da ake iya amfani da shi zuwa balaguro a ƙasashen duniya ba tare da fuskantar irin matsalolin da wasu ƙasashe kan yi fama da su ba saboda rashin ingantan fasfonsu zuwa matakin da Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Fararen Hula ta Duniya (ICAO) ta shata.
Nijeriya tana da fasfo mai shafi 64 da yake aiki na tsawon shekara 10 da aka samar musamman domin biyan buƙatar ‘yan ƙasa da ke zama a ƙasashen waje saboda a rage musu kai-komon sabunta fasfo a ofisoshin jakadanci. Ta wannan fuskar, NIS ta taimaki ‘Yan Nijeriya da sauran ‘yan ƙasashen waje masu zuba jari ta hanyoyi da dama ta yadda masu zuba jarin za su gamsu cewa Nijeriya ita ce ƙasa mafi daɗin gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari.
James Sunday, shi ne Kwanturolan NIS, reshen Jihar Ribas, ya rubuto daga Fatakwal.