Gwamna Dauda Lawal ya raba wasu motocin zirga-zirga ga rukunonin jami’an tsaron da ke aiki a jihar Zamfara.
Bikin ƙaddamar da rabon motocin tsaron, tare da motocin sufurin na ‘Zamfara Mass Transit’ ya gudana ne a filin Kasuwar Duniya da ke Gusau a yau Talatar nan.
- Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
- Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu yau a Gusau, ya bayyana cewa Babban Kwamandan Hukumar tsaro ta NSCDC, Dr. Ahmed Abubakar Audi, mni, OFR ne ya zama babban baƙo a wajen bikin.
Sanarwar ta Sulaiman ta ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta samar da motocin aiki guda 140 ga Hukumomin tsaro, wanda ke tabbatar da cewa har yanzu samar da tsaro ne babban abin da gwamnatin ta fi ba fifiko.
Cikin jwabin sa a wurin bikin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kasance tana gaggawar bayar da kulawa da gudumawa ga jami’an tsaron da ke aiki a jihar.
Ya ce, “Samar da motocin aiki ga jami’an tsaron zai bayar da ci gaba wajen sawwaƙa masu zirga-zirga, kai ɗauki a kan lokaci da ƙara ƙarfafa masu gwiwa wajen samar da tsaro da bin doka da oda.
“Wannan taro na yau, wani ci gaba ne na ƙoƙarin gwamnatina wajen ƙarfagawa, tare da inganta ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a duk faɗin jihar.
“Wannan kuma yana ɗamfare ne da alƙawuran da muka yi, tare da jajircewar mu wajen samar da duk abin da za mu iya don tunkarar dukkan nau’o’in rashin tsaro, samar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar mu.
“Wannan ƙoƙari namu yana ƙara nuna hobbasan gwamnatin mu wajen ƙarfafa wa jami’an tsaron mu don su samu sauƙin samar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar mu.
“Muna sane da muhimmancin ayyukan su wajen tabbatar da bin doka da oda don a samu cigababbiyar jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya.
“Saboda haka gwamnatina ta yi tsayin-daka wajen ganin an samar wa da jami’an tsaron nan, da duk goyon baya don su samu damar gudanar da ayyukan su cikin nasara.
“Ta bangare mu, mun kafa jami’an tsaron mu na kan mu, waɗanda muka sanya wa suna Jami’an Kare Al’ummar mu, Askarawan Zamfara, wato ‘Community Protection Guards.’ Mun yi niyyar tallafa wa ƙoƙarin ku, mu yi musayar ra’ayi, mu jawo al’ummar mu don kare ƙasar mu.
“A wannan taro namu na yau, mun shirya raba motoci guda 140 sabbi dal ga rukunonin jami’an tsaron mu da ke aiki a jihar nan. Waɗanda suka haɗa da A-kori kura mai gida biyu da motocin tsaro na Buffalo, duk mun samar da su ne don ƙarfafa wa jami’an tsaron da suka amfana.”
Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatin sa ta samar da motocin ba-bas sabbi guda 50 don inganta harkar sufuri a jihar.
“Wannan yana daga cikin tsarin mu na inganta harkar sufurin cikin gida da masu tafiya zuwa wajen jihar.
“Mun samar da kyakkyawan tsarin da zai tabbatar da kula da motocin, da kuma hana almubazzarancin da kuɗin da ake tarawa a harkar.
“Akwai na’urorin da aka sanya wa waɗannan motoci, waɗanda za nuna inda mota ta ke a kowane lokaci, an kuma sanya internet a cikin su domin fasinjoji.
“Kafin in kammala jawabina, zan girmama sadaukar da ran da Askarawan mu suka yi, waɗanda suka rasa rayukan su wajen kare martabar ƙasar mu, tare da iyalan da suka bari. Muna tuna ku a kowane lokaci, kuma muna girmama sadaukarwar ku.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp