Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanya hannu kan dokar haramta wa sarakunan gargajiya bayar da takardar izinin hakar ma’adanai a fadin jihar.
A yau Alhamis ne Gwamna Dauda, ya rattaba hannu kan dokar a zauren majalisar, gidan gwamnati, da ke Gusau.
- Minista Ya Ƙaddamar Da Shugabannin NIPR, Ya Jaddada Buƙatar Aiki Tare
- Kotu Ta Umarci A Sake Cafko Mata Dakta Idris Dutsen Tanshi
Babban mataimaki na musamman na gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne, ya bayyana haka a takardar da ya sanya wa hannun ga manema labarai a Gusau.
A cewarsa, dokar ta haramta duk wasu neman izinin hakar ma’adanai.
“Wannan ya hada da neman izini da ga mutane, kamfanoni ko kungiyoyi don hakar ma’adinai.”
A nasa jawabin, yayin da yake sanya hannu a kan wannan umarni, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa an yanke hukuncin ne saboda tsananin hatsarin da ke tattare da yawaitar fitar da takardun amincewa da hakar ma’adanai.
Ya ce: “A yau, a matakin da gwamnatina ta dauka na magance matsalar rashin tsaro, na sanya hannu kan doka da ta haramta wa sarakunan gargajiya bayar da takardar amincewa hakar ma’adanai a fadin kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.
“Kamar yadda babban mai shari’a ya bayyana, an gano ayyukan hakar ma’adanai a Zamfara a matsayin wani muhimmin al’amari da ke kawo tabarbarewar tsaro a jihar, musamman matsalar ‘yan fashin daji.
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi mana jagoranci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”