Sakamakon yawaitar rashin tsaro a Nijeriya musamman a yankin arewa ta sa gwamnoni da sarakunan gargajiya na yankin sun goyi bayan kafa ‘yansandan jihohi.
A ranar Talata da ta gabata ce, kungiyar gwamnonin arewa (NGF) suka gana da majalisar sarakunan gargajiya na arewa a Abuja, wanda sakamakon ganawar suka bullo da kudurin kafa ‘yansandan jihohi domin dakile matsalar tsaro a yankin da ma Nijeriya gaba daya.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa majalisar kasa ta dade tana watsi da kiraye-kirayen kafa ‘yansandan jihohi lokacin gyaran tsarin mulki, bisa fargabar gwamnonin na iya amdani da su ba bisa ka’ida ba.
Daga cikin matsaloli da aka tattauna a karshen wannan ganawa da ta gudana a otel din Transcorp Hilton da ke Abuja, ‘yan siyasan arewa da sarakunan gargajiya sun sake bibiyar matsalar tsaro a yankin arewa da sauran matsaloli da suka hana yankin ci gaba tare da kawo mafita da kuma goyon bayan yi wa tsarin mulki kuskwarima ta yadda za a samu damar kafa ‘yansandan jihohi.
Shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan Jihar Filato, Rt. Hon Simon Lalong shi ne ya karanta manyan batutuwan taron, inda ya bayyana cewa samar da ‘yansandar jihohi zai magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
A bangaren sakarunan gargajiya kuwa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III shi ne ya jaroranci sarakunan, wanda suka hada har da Shehun Borno, Sarkin Kano, Zazzau, Fika, Lafiya, Anka, Gumi, Attah Igala, Ochi Doma, Aku Uka na Wukari da dai sauransu.
Shugabannin dai sun bayyana cewa sun tattauna ne kan al’amuran da suka shafi tsaro da inganta rayuwar al’umma da noma da kasuwanci da zuba jari da nauyin da suka rataya a kan sarakunan gargajiya wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa.
Tattaunawar ta samu halartar wakilan kungoyoyin fararen hula da suka hada da Kungiyar Mata ta NFWP’ da ta bunkasa ilimin ‘ya`ya mata ta AGILE’, wanda dukkan su bankin duniya ne ya kafa su.
A halin da ake cikin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi matukar kokari wajen samar da tsaro da ababen more rayuwa.
Shugaban kasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa masu ruwa da tsaki jawabi a fadar gwamnatin Jihar Imo da ke Owerri bayan da ya kaddamar da babban hanyar Owerri zuwa Orlu da na Owerri zuwa Okigwe da sake gyaran ginin majalisar dokokin jihar da gwamna Hope Uzodimma ya yi.
Ya ce duk da karancin kudade da gwamnatinsa ta fuskanta ta samu nasarori masu dinbin yawa.
“Gwamnatina ta samu nasarar magance matsalolin ababen more rayuwa da na tsaro a Nijeriya idan aka kwatanta da shekarun da ke tsakanin 1999 har zuwa 2015 lokacin da muka karbi mulki,” in ji shi.
Shugaban Buhari ya yaba wa gwamnatinsa bisa kokarin magance matsalolin Boko Haram a yankin arewa maso gabas da inganta ababen more rayuwa wanda gwamnatinsa ta gada tun a lokacin zamanin mulkin PDP.
Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin Jihar Imo da na sauran jihohi domin samar da kyakkyawan dimokoradiyya wanda mutane za su yi alfahari da akidar jam’iyyarsu.
A nasa bangaren kuwa, shugaban kugiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ya bayyana cewa rashin tsaro da karancin ababen more rayuwa su ne babban matsaloli guda biyu da suke addabar yankin kudu maso gabashin Nijeriya. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokarin magance wadannan matsaloli guda biyu.