Kungiyar kwadago ta TUC, ta yi barazanar yin kwarya-kwaryar zanga-zanga tare da dakatar da al’umura, idan gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron yanar gizo da CBN ya fito da shi ba.
TUC ta yi barazanar ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ta hannun shugabanta Festus Osifo.
- Sojoji Sun Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutane Da Dama Tare Da Ceto Wasu AÂ Borno Da Kaduna
- Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Mako Guda A Turai
Kungiyar ta soki sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke son dora wa talaka.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne CBN ya fitar da wata sanarwa wadda ke neman a cire harajin kashi 0.5 cikin kan duk wata hada-hadar tura kudi da kwastomomi suka yi a yanar gizo.
CBN ya ce za ake amfani da kudaden da aka cire ne domin yaki da masu datsar bayanan mutane a harkar banki.
Sai dai wannan mataki ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya.