Fitaccen lauya nan mai kare haƙƙin bil’adama kuma mai lambar kwarewa ta SAN, Femi Falana, ya caccaki manufofin tattalin arziƙin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa sun ƙara jefa ƴan Nijeriya cikin talauci tare da kawar da aijin masu matsakaicin ƙarfi baki ɗaya sun koma talakawa.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Litinin, Falana ya bayyana cewa “tsauraran manufofin ƴan kasuwa” na Tinubu na ƙara dagula rayuwar al’umma. “Na ji yadda Shugaban ƙasa ke cewa gwamnoni su ‘jiƙa kasa’, amma gaskiyar magana ita ce rayuwa na ƙara tsanani ga talakawa,” in ji shi.
- Kotun Tarayya Ba Ta Da Hurumin Sauraran Karar Masarautar Kano – Falana
- Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Tinubu ya cire tallafin man fetur tare da buɗe kyale Naira ta kwace kanta a kasuwa, matakan da suka haddasa hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa gaba ɗaya. Falana ya soki yadda gwamnati ke bin tsarin IMF da Bankin Duniya ba tare da yin la’akari da illolinsa ga talakawa ba.
“Ina ganin tsarin rushe dukiyar kasa ta hanyar sayar da su ga ‘yan kaɗan ba zai rage bambancin wadata ba,” in ji Falana. Ya ce yawancin ‘yan Nijeriya ba sa iya samun abinci sau uku a rana, yayin da masu matsakaicin ƙarfi suka ɓace sakamakon waɗannan manufofi.
Falana ya buƙaci gwamnatin ta dawo da manufofin jin ƙai kamar shirin N-Power, GEEP, ciyar da ɗalibai a makaranta da bayar da tallafi ga marasa galihu. Ya kuma buƙaci gwamnonin jihohi su bi sahun ta tarayya wajen kafa waɗannan dokoki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp