Wasu manoma guda bakwai sun mutu nan take, bayan da tsawa ta sauka a kansu yayin da suke samun mafaka a karkashin wata bishiya.
Rahotanni daga Indiya, na cewa tsawa ta kashe mutane bakwai yawancinsu manoma a wani kauye da ke arewacin jihar Uttar Pradesh.
‘Yan sanda sun ce tsautsayin ya ritsa da manoman ne a lokacin da suke samun mafaka daga saukar ruwan sama a karkashin wata bishiya a ranar Talata.
Yanzu haka dai hukumomi jihar sun tabbatar da adadin mutane 49 wadanda tsawa ta yi ajalinsu a cikin mako guda.
Wannan ya sa gwamnatin daukar sabbin matakai na nuna wa mutane dabarun kare kansu daga tsawa.
A baya-bayan ma mamakon ruwan sama a yankin kudancin kasar, ya lalata gidaje da dukiyoyi masjmu tarin yawa.
Lamarin da ya sanya gomman mutane rasa matsuguninsu, wanda hakan ya sa aka shiga tallafa musu.