Ana kiwon tantabaru namiji da mace ne, sannan suna kasancewa a tare har zuwa iya tsawon rayuwarsu, suna kuma shafe shekaru daga 12 zuwa 15 suna rayuwa, inda namjin ne ke samo cifci, don gina musu gida.
Haka zalika, a kullum suke yin kwai kuma suna kai wa kimanin shekaru biyar suna yi, kazalika ana yi musu baye; macen da namijin, kana suna daukar daga kimanin kwana 17 zuwa 18 suna kyankyasar kwai.
- Da Ɗumi-ɗumi: Bayan CBN, FAAN, Manyan Ma’aikatun Hukumar Man Fetur Na Shirin Komawa Legas
- FCTA Ta Rushe Gidaje Dubu 15 Da Aka Gina Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Unguwar Gwarinpa Da Ke Abuja
Har ila yau, cikin ‘ya’yan tattabarun da aka kyankyashe na dauke da abincin da za su rika ci har zuwa kwana hudu, inda macen ke ciyar da ‘ya’yan daga kwana goma har zuwa lokacin da ‘ya’yan za su fara cin abinci da kansu, bayan kwana 26.
Matakan Fara Kiwon Tantabaru
Kiwon tantabara, sananne ne a Nijeriya; musamman a Arewacin wannan kasa ganin cewa, yara kanana su ma na da sha’awar yin wannan kiwo.
Har ila yau, tabbabara na nuna alamu na son zaman lafiya, inda hakan ya sa ake tashin su a wasu bukuwa na wanzar da zaman lafiya a fadin duniya.
Haka zalika, da dan karamin jari za ka iya shiga wannan harka, duk da cewa; an fi saurin samun riba idan aka rungumi fannin ta hanyar amfani da kayan kiwo na zamani; sabanin na gargajiya.
Mahimmancin Kiwon Su:
Daga watanni biyar zuwa shida; sun fara yin kwai, sannan kuma ba su da wata wahalar sarrafawa wajen kiwo, don haka za iya kiwata su har a bayan daki, idan kuma suka kai kimanin kwana 18, sai su fara kyankyasar kwai.
Daga sati uku zuwa hudu, za ka iya cin naman ‘ya’yan; haka nan idan ka zuba jari kadan, za ka samu riba mai yawa.
Wannan kiwo, ya kasance yana samar da kudaden shiga masu yawa ga wadanda suka rungumi wannan fanni a kasashe kamar Bangaladash, Indiya, Nijeriya, Pakistan da sauransu.
Wajen Kwanansu:
Ya na da kyau ka sama musu gurin kwana mai kyau tare da gina musu daki mai tsawo, don ba su kariya daga kai harin musamman muzuru, kare da sauran dabbobi masu illa, haka nan, a kuma tabbatar da dakin na samun shigar wadatacciyar Iska tare da sanya fitila.
Har wa yau, za ka iya gina dakin da katako ko ka yi na kwali, domin kuwa kowace tattabara na bukatar sararin da ya kai kimanin tsawon mita 30 da kuma fadin mita 30 a waje. Haka na, yana da kyau a rika tsaftace dakinsu, akalla sau biyu a wata ko a kullum, sannan ana so abincinsu da ruwan shansu, ya kasance a kusa da dakinsu.
Ciyar Dasu Abinci:
Bugu da kari, tattabaru sun fi cin Alkama, Masara, Shinkafa da sauran dangoginsu, ana kuma so mai kiwon su ya tabbatar ya ajiye musu abincinsu a kusa da dakinsu na kwana, ana kuma so abincin nasu ya kasance mai gina jiki, musamman don idan sun ci su girma da wuri tare da samun koshin lafiya.
Haka nan, ana so mai kiwon nasu ya tabbatar da tukunyar ruwansu ta na sha na kusa da dakinsu na kwana tare da kula da tsaftarsa.
Lokacin Fara Kwansu:
Macen tantabara na fara yin kwai, bayan ta kai wata biyar zuwa shida, sannan kuma tana yin kwan ne duk bayan wata guda, macen da namijin ne ke kyankyashe kwan daya bayan daya, har ila yau, suna kai wa kwana daga sha bakwai zuwa sha takwas suna wannan kyankyasa.