Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da haɗin guiwar Tsofaffin ɗaliban Sashen Nazarin Kimiyyar Harshe na Jami’ar Bayero Kano ajin shekara ta 2015 ta miƙa sakon godiya ga Masarautar Hausawan Turai da ke birnin Paris na ƙasar Faransa da Mai Martaba Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajou Djankaɗo, bisa naɗi ɗan wannan ƙungiya kuma shugabanta, Alhaji Hassan Baita Ubawaru a matsayin Ma’ajin Hausawan Turai a ranar Lahadi 14 ga Yulin 2024.
Sakataren ƙungiyar, Muhammad Bashir Amin ne ya aike da wannan saƙon a madadin kungiyar ga Masarautar Hausawan Turai da Mai Martaba Alh. Sirajou Djankaɗo a wajen taron walimar taya murna da karramawa da abokan Mai girma Ma’ajin Hausawan Turai suka shirya masa a birnin Kano a ranar Litinin 29 ga Yulin 2024.
- Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
- Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani
A jawabin na Muhammad Bashir, ya ce tabbas an ajiye ƙwarya a gurbinta bisa zaɓo mutum mai nagarta da amana da hidimtawa a al’umma irin Alh. Hassan Baita Ubawaru, a wannan matsayi kuma uwa uba daman shi Hassan ɗin masani ne a fannin ilimin harshe da adabi da al’adun Hausawa don kuwa ya samu shaidar digirinsa na farko a harshen Hausa.
“Haƙiƙa an karrama mu kuma mun ji daɗin wannan karamcin ƙwarai da gaske, kuma ƙungiya za ta ci gaba da ganin wannan karamcin har abada, za kuma mu kyautata alaƙa mai kyau da wannan Masarauta ta Hausawan Turai ta fuskar bunƙasa harshe da adabi da al’adun Hausawa da taimakon mabuƙata ” cewar Muhammad Bashir.
Sakataren ƙungiyar a ƙarshe ya aike da sakonsa na taya murna a madadin mambobin kungiyar ga sabon Ma’ajin Hausawan Turai, Alh. Hassan Baita Ubawaru, bisa naɗa shi a wannan matsayi na sarauta mai girma da Allah ya sa ya zama mutum na farko a tarihi da aka naɗa a Masarautar Hausawan Turai.
Bashir ya yi fatan Ma’ajin Turai ya ninka ayyukansa na alheri da ya saba da kuma yin haƙuri da hidimar jama’a da taimakon mabuƙata, ya kuma yi addu’ar Allah ya kama masa, ya taya shi riƙon kafa tarihi na alheri a wannan Masarauta mai girma.