Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP. Ya ce, “Ina ganin Jonathan zai karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya saboda mutum ne mai son cigaban jiharsa. Duk da maganganun da ake yi kan zai tsaya takara, bana ina ganin zai yi kuskuren hakan saboda lokaci ya riga ya wuce.”
- Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole
- Ko Jonathan Zai Iya Ja Da Tinubu A 2027?
Ya ce, tun bayan barin ofis a 2015, tasirin siyasar Jonathan ya ragu, kuma babu wani alamar da ke nuna yana son komawa cikin harkar siyasa kai tsaye. “Bai nuna wata alama ta shiga siyasa ba, tun bayan barin mulki,” in ji shi.
Sunny-Goli ya ƙara da cewa tsohon shugaban ya fi dacewa ya ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan zaman lafiya da hulɗa da ƙasashen duniya maimakon komawa cikin rigimar siyasa a gida, musamman a yayin da ake ganin yanayin siyasa a Bayelsa na ya sauya.