John Ayuba, wanda ya tsaya takarar mataimakin gwamna a Jihar Kaduna ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya fice daga jam’iyyar kuma ya komawa jam’iyyar ADC.
Ayuba ya sanar da ficewarsa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP na unguwar Unguwan Gaiya da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
- An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
- Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Ya ce ya bar PDP ne saboda rashin jagoranci na gari a matakin ƙasa, inda ya zargi wasu shugabannin jam’iyyar da lalata makomar PDP da kuma yin aiki da gangan don hana jam’iyyar nasara.
Ayuba ya ƙara da cewa PDP ta kasa ɗaukar mataki kan waɗanda suka hana jam’iyyar cin nasara a zaɓen 2023, lamarin da ya rage wa mambobin da suka jajirce ƙwarin gwiwa.
Ya ce bayan yin shawarwari da magoya bayansa, ya yanke shawarar cewa ci gaba da zama a PDP ba zai yi masa amfani ba.
Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp