Wata kotu dake birnin Manchester na kasar Ingila ta bayyana cewa, an samu gawar tsohon zakaran damben duniya Ricky Hatton a rataye a gidansa yayin da aka bude shafin shari’arsa kwanaki kadan da mutuwarsa, a ranar Alhamis da ta gabata, wata kotu da ke binciken mutuwarsa ta bayyana samun cikakaken rahoto dangane da tsohon dan damben.
Kocinsa Paul Speak ne ya gano gawar Hatton mai shekaru 46 da ake yi wa lakabi da “Hitman” a ranar 14 ga watan Satumba a gidansa da ke Greater Manchester, kamar yadda kotun Manchester South Coroner ta shaida wa manema labarai, kotun ta saurari cikakkun bayanai game da gano gawar Hatton da jami’in dan sanda Alison Catlow ya bayar, dangin tsohon dan damben na Burtaniya, wanda ya lashe kambun duniya a ajin masu nauyi da mara nauyi, sun bayyana cewar sun yi masa ganin karshe a ranar 12 ga watan Satumba.
Amma washe gari bai halarci wani taron ba kamar yadda aka yi tsammani, a safiyar ranar 14 ga wata manajansa ya isa gidansa don kai shi filin jirgin sama na Manchester don hawa jirgi zuwa Dubai, amma sai gawar Hatton ya samu a rataye cikin dakinsa.
An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila.
Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton.