Kwanan baya, tsohon firayin ministan kasar Belgium Yves Leterme, ya yi tsokaci yayin da yake zantawa da wakiliyar CMG cewa, yanzu huldar dake tsakanin Amurka da kasar Sin, da huldar dake tsakanin kungiyar tarayyar Turai ko EU da kasar Sin, dukkansu sun shiga wani lokaci mai muhimmanci.
A bangaren EU, ya dace ta nace kan matsayar kanta, a maimakon kasancewa ‘yar koren Amurka, wato akwai bukatar ta bayyana ra’ayinta a fili. Kuma kamata ya yi EU da kasar Sin su ci gaba da ingiza hadin gwiwa ba tare da rufa rufa ba, da gudanar da cinikayya mai adalci tsakaninsu, ta yadda za su samar da wani muhalli mai inganci ga kamfanonin sassan biyu, tare kuma da ba da kariya ga zuba jari da musaya dake tsakaninsu.
Game da ra’ayin da aka nuna wai raba kai da kasar Sin domin rage hadari, Leterme ya bayyana cewa, raba kai ba matakin da ya dace da a dauka ba, duk da cewa, kasashen duniya suna kokarin kare manyan hakkokin kansu, amma bai kamata a dauki matakin ba da kariya ba. Ya dace a bude kofa ga juna, kuma a kara karfafa cudanya tsakanin kasa da kasa, ta haka ne za a iya sassauta hadarin musayar tattalin arziki yayin kare moriyar kansu. (Mai fassara: Jamila)