A yau litinin ne, tsohon firaministan kasar Kenya, Raila Amolo Odinga ya iso Nijeriya domin halartar taron shekara-shekara da jaridar LEADERSHIP ta saba gudanarwa.Â
Odinga, ya sauka ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Ya iso kasar ne, kafin a fara gudanar da taron na jaridar LEADERSHIP karo na 14 wanda za a karrama wasu manyan mutane.
Za a gudanar da taron ne, a ranar 31 ga watan Janairu a babban birnin tarayya, Abuja.
Odinga, shine babban bako mai magana a taron yayin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zai jagoranci zaman.
Fitaccen kwararren dan siyasar ya iso Nijeriya ne da misalin karfe 12:10, inda mahukuntan jaridar LEADERSHIP da wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya suka tarbeshi.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, tuni tawagar tsohon Firaministan ta iso Nijeriya a ranar Lahadin da ta gabata.