Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.
Majiyoyi sun ce ficewarsa ta biyo bayan rashin gamsuwa da tafiyar jam’iyyar. A cewar El-Rufai, APC ta kauce daga ainihin manufofinta, don haka ba zai ci gaba da kasancewa a cikinta ba.
- Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
- Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Koma wa SDP ya haifar da raɗe-raɗin cewa yana shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, lamarin da ke nuna sauyar tsarin siyasa a Nijeriya, idan har za a samu ɗan takara daga arewa a 2027.
A halin yanzu, shugabannin APC na nazarin tasirin wannan sauyi, yayin da SDP ke maraba da zuwansa a jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp