• English
  • Business News
Wednesday, May 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni

by Muhammad
1 year ago
in Da ɗumi-ɗuminsa, Manyan Labarai
0
Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bayan kai ruwa rana, daga karshe dai tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince ya mika kansa a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ranar 13 ga watan Yuni kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) take yi masa kan almundahanar makudan kudade.

Lauyan da ke tsayawa, Yahaya Bello, Abdulwahab Mohammed, ya yi wa mai shari’a Emeka Nwite, alkawari a ranar Juma’a, bayan kotun ta ki amincewa da bukatar dakatar da shari’ar da wanda ake kara ke yi.

  • Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo
  • Zan Yi Murabus Matukar Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba – Shugaban EFCC

Muhammad ya ce tsohon gwamnan baya tsoron a gurfanar a gaban kotu ko kadan.

Lauyan tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa, rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana a Abuja, don haka ya yanke shawarar buya don tsira da rayuwarsa.

Alkalin ya ce Bello ba shi ne tsohon gwamna na farko da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi kadai ba, kuma ba zai zama na karshe ba.

Labarai Masu Nasaba

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

Alkalin kotun ya kuma ce ana tuhumarsa ne kan zargin da ba a tabbatar da shi ba, inda ya kara da cewa doka ma tana daukar duk wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifin.

A karshe dai Mai shari’a Nwite ya sanar da ranar 13 ga watan Yuni don Yahaya Bello ya gurfana a gaban kotu domin fara sauraran kara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: EFCCKogiKotuYahaya Bello
ShareTweetSendShare
Previous Post

GORON JUMA’A

Next Post

Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci

Related

Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?
Manyan Labarai

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

49 minutes ago
Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
Manyan Labarai

Gwamnan Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar

15 hours ago
Wata Mata Ta Kashe Dan Hayar Da Ke Gidanta A Ondo
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC A Ondo, Sun Nemi N100m

18 hours ago
Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Bai Wa Ɗan Arewa Takara A 2027
Siyasa

Wike Ya Gargaɗi PDP Kan Bai Wa Ɗan Arewa Takara A 2027

24 hours ago
Nijeriya Ta Biya Dukkanin Bashin IMF Na COVID-19
Manyan Labarai

Nijeriya Ta Biya Dukkanin Bashin IMF Na COVID-19

1 day ago
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5, Sun Kwato Makamai A Borno

2 days ago
Next Post
Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci

Motocin Sabbin Makamashi Kirar Kasar Sin Sun Mamaye Duniyar Motoci

LABARAI MASU NASABA

Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?

Kotu Ta Ce Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje Kan Zargin Aikata Rashawa A Kano

May 14, 2025
Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi

May 13, 2025
Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

Tsaro: Gwamna Lawal Ya Raba Motoci 140 Ga Jami’an Tsaro A Zamfara 

May 13, 2025
Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci

May 13, 2025
Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe

May 13, 2025
Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka

May 13, 2025
Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci Sake Tura Sojoji Cikin Gaggawa Zuwa Borno Da Yobe

May 13, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Brazil

May 13, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

May 13, 2025
An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya

May 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.