‘Yan bindigar sa suka sace tsohon mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado, sun sake shi bayan an biya kudin fansa Naira miliyan hudu.
Wata majiya daga ‘yan uwansa ta bayyana cewa an saki Farfesan ne a kewayen tsaunukan da ke tsakanin kananan hukumomin Akwanga da Nasarawa Eggon a jihar a daren ranar Lahadi.
- An Haramta Wa Limamai Karanta Alkur’ani Daga Waya A lokutan Sallolin Dare A Kuwait
- Rashin Tsaro: Buhari Ya Gyara Nijeriya Fiye Da Yadda Ya Same Ta, In Ji Adesina
An yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan ne a daren ranar Alhamis din da ta gabata a gidansa da ke Rinza, Wamba a Karamar Hukumar Wamba ta jihar.
Tun da farko wadanda suka sace shi sun bukaci a biya su Naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa amma ‘yan uwansa suka roki a rage kudin zuwa Naira miliyan biyu.
Daga baya ‘yan uwan nasa suka tara kudin zuwa Naira miliyan 3.5 amma maharan suka ki karbar kudin har sai da suka kai miliyan hudu.
“Sun karbi kudin fansar ne a kusa da makarantar Sakandiren Mada Hills da ke Akwanga, da katin waya na N200, sannan suka sake shi a kusa da Angwan chiyawa, kusa da tsaunukan da ke tsakanin Akwanga da Nasarawa Eggon,” in ji wata majiya daga iyalinsa.
An tattaro cewa an kai Gye-Wado zuwa fadar mai martaba Sarkin Wamba, Oriye Rindre, Lawal Musa Nagogo, bayan an sake shi.
Wani tsohon shugaban kungiyar NUJ kuma tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Dogo Shamma, ya tabbatar da sakin Farfesa Gye-Wado, ta hanyar wani sakon da ya aike wa majalisar NUJ ta kafar WhatsApp da misalin karfe 10:06 na dare.
“Cikin ikon Allah an sako Farfesa Onje, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane a yanzu,” in ji sakon.