Hakimin Kurfi a Jihar Katsina kuma tsohon sakataren Hukumar FEDECO, Alhaji Ahmadu Kurfi, ya rasu yana da shekaru 93.
An haifi Kurfi a shekarar 1931, kuma ya riƙe sarautar Maradin Katsina a Masarautar Katsina.
- Shugaban Kasa: ACF Za Ta Goyi Bayan Ɗan Takarar Arewa A Zaɓen 2027
- Shugabannin Arewa Na Baya Sun Gaza – Uba Sani
Ya yi ayyuka da da dama inda ya rike matsayin jami’in gwamnati, daga baya ya zama mataimakin babban sakatare a Ma’aikatar Tsaro yayin juyin mulkin 1966.
Sannan daga baya ya zama babban sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati.
Kurfi shi ne ya fara rike muƙamin sakataren hukumar FEDECO, wadda ta shirya zaɓen 1979 da ya kai Alhaji Shehu Shagari ga zama shugaban ƙasa.
Cikakken bayani na tafe.