Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, kuma ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Barista Ibrahim Kashim, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban jam’iyyar a mazaɓarsa ta Majidadi, ranar 21 ga watan Yuli, 2025, Kashim ya bayyana cewa ya fice daga PDP, amma bai bahhana dalilin ficewarsa ba.
- Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
- Shirin Ba Da Horo A Kasar Sin Ya Taimaka Wa Inganta Masana’antar Gyadar Senegal
Ya rubuta cewa: “Bayan yin la’akari da lamarin sosai, ina so na sanar da ku cewa daga yau, na fice daga jam’iyyar PDP. Zan ci gaba da neman hanyar da zan yi wa al’umma hidima da sadaukarwa, gaskiya, amana da kuma tsoron Allah (SWT).”
Kashim ya gode wa shugabannin jam’iyyar a mazaɓarsa bisa damar da suka ba shi na zama ɗan jam’iyyar, wacce ta ba shi damar tsayawa takarar gwamna a zaɓen 2023.
A shekarar 2023, kafin babban zaɓe, Kashim ya janye takararsa don bai wa Gwamna Bala Mohammed damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Ya ce ya zagaya dukkanin ƙananan hukumomin Jihar Bauchi domin goyon bayan Gwamna Bala yayin yaƙin neman zaɓe, duk da cewa yana ci gaba da aiki a matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha.
A watan Janairu 2025, Kashim ya yi murabus daga matsayin SSG, inda ya ce gwamnan ne ya umarce shi da yin hakan.
Rahotanni na nuna cewa Kashim na da niyyar sake tsayawa takarar gwamna a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp