Gwamna Dauda Lawal ya bayyana tabbatar da nasarar da ya samu a zaben gwamnan Jihar Zamfara.
Gwamna Dauda Lawal ya yi nasara a zaben Gwamna da aka yi a watan Maris, inda ya ya yi nasara kan gwamna mai ci a wancen lokacin da gagarumar nasara.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Gusau, ya jaddada cewa hukuncin kotun yana wakiltar ra’ayi da shawarar mutanen Zamfara kan zabinsu Dauda Lawal.
Talla