Tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya rasu a yau ranar Lahadi 13, ga Yulin 2025.
Wani gajeren saƙo da Garba Shehu, mai taimaka masa a ɓangaren yaɗa labarai ya fitar da yammacin yau Lahadi, ya tabbatar da cewa Buhari ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.
- Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
- Shettima Ya Ziyarci Buhari A Landan Cikin Sirri Don Duba Lafiyarsa
Shehu ya rubuta sanarwar kamar haka: “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UUN. Iyalan tsohon shugaban ƙasa sun sanar da rasuwar Muhammadu Buhari, GCFR, a yau da rana a wani asibiti da ke London. Allah ya karɓi ransa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus. Amin.”
Sanarwar mai sanye da kwanan wata: 13 ga Yuli, 2025.
Babu cikakken bayani kan musabbabin rasuwar, amma Buhari ya daɗe yana zuwa Birtaniya don samun kulawar likita tun yana shugaba har bayan saukarsa daga mulki.
Buhari, wanda tsohon janar ne a rundunar sojin Nijeriya, ya shugabanci ƙasar a matsayin shugaban soja daga 1983 zuwa 1985, sannan ya dawo a mulkin dimokuraɗiyya a 2015, bayan shekaru 30. Shi ne ɗan adawar farko a tarihin Nijeriya da ya kayar da shugaban ƙasa mai ci a zaɓe.
Zuwa yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a gudanar da jana’izarsa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp