Tsohuwar ministar kula da ayyukan jin-kai da ci gaban al’umma, Sadiya Umar-Farouk, ta ki amsa goron gayyatar da Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Kasa Zagon Kasa (EFCC) da ke Abuja, don amsa tambayoyi kan zargin Almundahanar Naira biliyan 37.1.
Wata majiyar EFCC ta shaida wa Leadership Hausa cewa tsohuwar ministar ta yi watsi da gayyatar da hukumar ta yi mata.
- Masu Fyade Da ’Yan Luwadi 369 Aka Kama A 2023 A Katsina
- Mutane 6,000 Sun Amfana Da Zakka Ta Miliyan N132 A Masarautar Hadejia – Kakakin Masarautar
Majiyar ta ce Sadiya ba ta bayyana ba kuma lauyanta bai wakilce ta ba.
Sadiya ta yi minista a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga watan Agustan 2019 zuwa Mayu 2023.
A makon da ya gabata ne EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar biyo bayan wani bincike da aka kaddamar kan ayyukanta a lokacin da ta rike mukamin minista.
Ana bincikenta ne kan kudi Naira biliyan 37.1 da ake zargin sun yi batan dabo karkashin kulawarta, ta hannun wani dan kwangila, James Okwete.
Hakan ya sa EFCC ta bukaci tsohuwar ministar da ta gurfana a hedikwatarta da ke Jabi, a Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.
Sai dai ba ta bayyana a hedikwatar EFCC din ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp