Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da irin mazan da ba sa barin matansu su fita su yi aiki ko da kuwa sun kammala karatunsu, shin kishi ke janyo hakan ko sabanin haka. Da yawan mazaje na hana matayensu fita zuwa aiki ko da kuwa sun samu aikin da suke bukatar yi, amma mazan sai su ki barin matan nasu.
A tawa fahimtar rashin hanawar ga wasu mazan suna yi ne bisa wasu dalilai, wanda kuma ciki har da kishi. Wasu mazan na hana matansu yin aiki ne ta dalilin zafin kishin da suke da shi, gudun ka da ta fita ta hadu da wani namijin ko kuma kar ma tayi magana da wani namijin a wajen aikin, idan ya auna ya ga hakan ba zai taba yuwa ba muddin za ta yi aikin dole ne tayi magana da wasu mazan daban sabida tsarin aikin sai ya hanata, maganin kar ayi ma bare a fara, shi dai burinsa kawai muddin zai barta toh dole ne a samo wajen aikin da babu namiji ko daya a ciki, wanda a yanzu a wannan lokacin abu ne mai matukar wahalar gaske ya tsaya neman hakan muddin kuwa aikin za ta yi.
Wasu kuma mazan suna hana matansu aiki ne ya yin da suka fuskanci yanayin matan nasu za su iya canjawa a duk lokacin da suka fara aiki daga mutane na gari zuwa mutanen da ba na gari ba, sai mazan su hana su yin aikin. Wasu kuma mazajen ra’ayinsu ne a haka basa bukatar barin matan nasu aiki a ganinsu mace me aure ba ta dace da fita aiki ba, a ganinsu kamar an sauka daga tsarin musulunci ne, kowa da irin nasa fahimtar.
Wasu kuma suna kallon barin mace yin aiki hakan ba al’adar malam bahaushe ba ce su lokacinsu basu taso sun ga ana yin hakan ba. Wasu kuma suna hana matansu yin aiki ne sabida suna tsoron ka da abin da sukaiwa matan wasu ko ‘ya’yan wasu ya faru akan matansu sabida mukamin da suka rike matsayinsu na manya masu kula dana kasansu ba mamaki sun yi wa yaran wasu ko matan wasu barazanar wani abun ko akan aiki ko wani abun na daban da suka rinka neman bukatarsu wajenta suna amfanin da mukamin da suke da shi dan sun gansu a can sama.
Wasu kuma suna barin matansu ko da kuwa macen ba ta bukatar yin aikin za su tirsasata tayi sabida sanin mahimmancin aikin. Dalilai da dama kowa da irin nasa ra’ayin, kuma kowa da tasa hujjar. Sai dai kuma abin da wasu ba sa tunawa da shi shi ne; ko da ace mace ba ta aiki kullum tana zaune a cikin gida, hakan ba zai sa taki canja dabi’arta ba muddin tana da wannan niyyar a zuciyarta.
A kowanne abu, kuma a kowanne irin aiki akwai nagari akwai na banza, kamar dai yadda yake a mu’amulance ta fannin zamantakewar rayuwa, ana samun nagari ana samun batagari.
Haka kuma duk macen da ta so ta lalace za ta lalace, duk macen da ba ta so ta lallace, ba za ta lalace ba ko da kuwa kullum za ta fito titi tana yawo, sai dai kaddara wadda ta riga fata in ji masu iya magana. Wannan kadan kenan kuma a takaice. Dalilin haka ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala, inda suka fayyace na su ra’ayoyin kamar haka:
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Ni a nawa tunanin kishi ne ko kuma rashin yadda da nutsuwar matar dari bisa dari, wasu matan sukan ce wai bakin ciki ne, ni a nawa hangen duk mutumin da ya ajjiye ka a gidanshi matsayin uwar ‘ya’yanshi babu zancen bakin ciki, kawai kishi ne, wani kawai haka yake ya na da bakin kishi. Wani kuma kamun kanki ne bai yadda da shi ba, watakila daman ya san dabi’unki tun kafin auren, zai ga kamar abun da za ki je ki ci gaba da yi kenan. Aiki ya na da amfani sosai ga ‘ya mace, ko da ace mijin yana iya dauke dawainiyar gidanshi, dole aikin zai taimaka masa ta wasu bangarorin, kamar yawan bani-bani, ko kuma wani abun da zai taso a gida mijin ba ya nan, ko biki ko suna ya taso za ta yi hidimar ta ba tare da ta jira mijin ba, sannan kuma uwa uba idan mace tana aiki ko mijin mutuwa yayi ya bar ma ta yaran za a samu sauki sosai, ni idan ni ce mijna ya nuna ba ya son nayi aiki, zan tsaya in yi nazari ne na gani, zai iya dauke nauyin gidan, idan na ga ba zai iya ba kuma ina son aikin, toh hakura da auren shi ya fi, saboda a karshenta zai zo ya kasa rike gidan, gashi ke kuma kin bar dama ta wuce ki, idan na ga kuma zai iya, sai kuma na duba girman son aikin a zuciya ta, idan son mijin ya dannen son aikin toh zan hakura na zauna ne kawai, domin babu amfani ka matsa dole sai ka yi, duk irin fahimtar da shi din da za ka yi ba zai goge mishi abun da yake gani a zuciyar shi ba nakin aikin, idan aka kuskura aka taro dake da iyaye har ya amince dole, irin shi ne ake samun matsala, sai ka ga a gida babu kwanciyar hankali a wajen aikin ma babu, kamar misali; kullum yana korafin baki dawo da wuri ba, ko ya ce kafin ki fita kimin kaza, ko kina gurin aikin yana bibiyarki, hakan zai sa macen ta zama ba ta da nutsuwa Sam!, tsirfa iri-iri za ki ga yana kirkiro da su. Toh ni dai shawarar da zan bawa maza shi ne; kafin su auri mace su samu fahimtar juna sosai, ba sai na ce wa namiji wai aiki na da amfani ga mace ba, sun san amfaninsa, kishi ne yake sa su kin aikin, yana da kyau ya kasance mijin yana wa matar shi yadda da ita kanta ba tai wa kanta saboda tsare mutuncin kanta da take yi, idan har akwai irin wannan amincewar babu maganar hana aiki.
Bazazzagin Me Iyali daga Zariya:
Maganar gaskiya ban ga amfanin hana ‘ya mace yin aiki ba idan har za ta kasance me kare mutuncinta da kuma hakkin mijinta, idan har akwai gaskiya da amana barin ta yin aikin shi ne Mafi kyau. Aikin ‘ya mace Musanman a gidan mijinta yana da matukar amfani ka ma daga al’amarin yau da kullum, kananan hidimomi kai har ma da wasu manya-manyan a cikin zamantake wa na auratayya.
Na’am! Tabbas ko da ace mata ta ba ta da ra’ayin aiki sai na tilasta ma ta yin aikin ko kuma ta sa mi sana’ar hannu me karfi. Shawara ta akan masu hana matar su yin aiki ina ga hakan kuskure ne babba matukar yin aikin na ta ba yana da nasaba da keta haddinta da kuma gaza kare hakkin auratayya ba, domin yin aikin ta zai samar ma ka da sauki Musanman ta hanyar yawan bani-bani duk da cewar hakki ne a wuyanka.
Zahra’u Abubakar Dr Zara Karamar Hukumar Nassarawa Gama-D Jihar Kano:
A nawa fahimtar dai ina ganin kishi ne yake hana wasu mazan kin barin matayensu su yi aiki wasu kuma mugunta ce da keta take hana su su bar matansu aiki, wasu kuma tunanin rashin iya kame kai da nutsuwar matan a gun aikin shi suke tsoro gaskiya, amfanin yin aiki ga ‘ya mace abu ne me matukar muhimman ci saboda akwai ayyuka da dama waanda ba za su tafi ba sai dai macen, musanman bangaren aikin asibiti a kasar hausawa da dai sauransu sannan kuma bangaren zamantakewa duk da dai hakkin mijin ne yin abubuwa dai-dai gwargwadon karfinsa, amma idan mace na aiki tabbas! dole akwai taimakon juna kama daga gishiri, ankon biki, gudunmawa da dai sauransu. A gaskiya idan ni ce Mijina ba ya san na rinka fita aiki musanman irin aikina na asibiti to zan kwantar da kai ne in rinka nuna masa muhimmancin fita aikin zan je ne in taimaka ga mara sa lafiya, musanman ‘yan uwana Mata ka ga bai kamata mu Mata muna da sanin aikin ba kuma ace maza ne ke kula da Mata ‘yan uwanmu ba, sannan kuma fitar nan za ta ke rage min kewa ma’ana za ta sa in dan zama ‘Busy’ na dawo dole akwai gajiya zan so in huta sannan in kama aikace aikace na na gida ka ga wasu gulma ce- gulma ce da bin makota duk ba abun da ya shafe ni bane, sannan abun da bai kai ya kawo ba bai kamata in jira ka ba saboda yau da gobe ba gazawa kai ba, amma zan so ni ma in rinka tabuka wani abun ko da kuwa da kudin me kwasar shara ne ni ma in sami lada. Shawarar da zan bawa maza akan amfanin aikin ‘ya mace shi ne a takaice dai aikin ‘ya mace aiki ne me matukar muhimman ci ga su kansu matan da kuma su kansu mazan mussanman ma a irin wannan zamanin da idan ka hana mace aikin ma to tabbas wataran daka Kai matar ka inda ake ya kamata ace mace ‘Yar uwarta ya kamata ta yi aikin, amma sabanin irin ka daba ka bar taka ta fito ta yi ba sai ka ga Namiji shi ne akan iya yinka dole shi za ta gani, so matukar za a bawa juna amana kowa ya rinka tuna makomar sa to tabbas yin aikin ya mace yafi rashinsa Alkhairi.
Hussy Saniey:
Gaskiya wannan ba kishi bane, saboda ai tana fita unguwa, biki, suna, da dai sauransu. Saboda haka maganar kishi ma bata taso ba, wani dai ra’ayinsu ne daban. Amfanin aikin ‘ya mace ai ba zai lissafu ba, domin duk abin da za ta samu a hidimarta da ta yaranka za ta kare, kai wa ta ma har sutura take dinka wa mijin bayan kayan abinci da za ta taimaka maka da shi. Eh! zan iya barinta saboda aikin yana da matukar amfani gare ni da yarana. A matsayina na mace idan maigidana ya hana ni aikin zan ta lallashin shi har Allah ya sanya na dace. Shawarata anan ita ce maza su daure don Allah suna barin matansu aiki domin dai aikin nan amfanin kanku ne duka, saboda za ta dauke maka wasu hidindimun da suka rataya a kanka, wanda idan da bata aikin dole kai ne za ka yi ma ta su, to ko dan rage maka nauyin da take ya kamata a yi hakuri a rinka bari ana aikin.
Raheenat Mamoudou Jihar Niamey:
Ni dai a ganina tsakani da Allah maza basa kyautawa idan sun ce matayensu ba za su yi aiki idan sun yi aure, zan iya kiran wannan abin da tauye hakki da kuma wani nufi na daban a zuciya, babu wani kishi wasu kam nasu zalinci ne tsantsa da nuna iko. Aiki wajen mace ya na da amfani matuka wajen diya mace, zai taimaka ma ta wajen magance wasu matsalolinta, za ta kuma taimaki mahaifanta da kuma ‘yan uwanta da abokan arziki hatta shi mijin za ta taimaka mishi idan ya shiga wani yanayi. Al’umma da yawa za su amfani da wannan ilimin nata ba kadan ba. Kafin mu yi auren ma sai mun yi yarjejeniya a gaban shaidu, babu yadda za a yi na auri mijin da zai hanani aikina, iyayena sun sha dawainiya a kan karatuna har na kammala babu yadda za a yi wani can ya nemi ruguje min farin cikina. Maza Ku ji tsoron Allah ku daina tauye hakkin matayenku ta hanyar nuna musu gadara da iko wajen hana musu aiki tsabar mugunta, a lokacin da aka sakata ‘school’ iyayenta suna shan wahala a kanta kana ina? Babu namijin da zai yi tunkaho ya ce zai iya biya wa matarshi duk wasu bukatunta ko ya yi rantsuwa karya yake, yau da gobe sai Allah babu abin da ya ke haddasa tsana da kuma kiyaye sai yawon roko da kuma bani-bani, amma idan mace tana aikinta kai kanka oga karuwarka ne saboda za ta yi abubuwa da yawa ba sai ta tambayeka ba namiji mai hankali kawai zai gane wannan, Allah ya sa mu dace ya zamana mazaje masu tsoron Allah wadanda za su kaunaci farin cikinmu ameen, dan Alfarman Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.
Hafsat Yusuf Muhd daga Jihar Kano
unguwar Gadon Kaya Hauren Legal:
Dalilin da yasa wasu mazan ba sa barin matansu yin aiki sabida wasu matan ba suda kamun kai, wani kuma yana ganin ya dauke ma ta komai me za ta yi da aiki?, wani kuma ba shida burin aiki a rayuwarsa sai ya rinka tunani ko ya kasa yi ma ta komai ne, wani kuma ko bai dauke komai ba to shi fa bai yarda da aiki ba. Aikin ‘ya mace ya na da mutukar mahimmanci, sabida amfaninsa za ta taimakawa gida idan babu wani abun za ta siya ba sai ta ce miji ya kawo ba, ko akan yaransa za ta taimaka ko rashin lafiya, ko biki ko suna ba sai ta tambayi kudin mota ba za ta yi wa kanta da wasu sauran matsalolin gida. Eh! sabida za ta taimakawa gidan za ta rage wasu matsalolin gidan ko ba shida kudi ko kuma baya nan kamar asibiti makaranta da sauransu. Aikin ‘ya mace yanada mahimmanci sosai sabida rayuwa ta sauya sosai, za ta rinka taimakawa mai gidanta nesa ba kusa ba. Saboda haka maza ku yi hakuri ku bar matanku su yi aiki sai mu rufawa kai asiri baki daya na gode sosai.
Auwalu Abdullahi Umar Kiru:
Shi aikin mace wani nau’i ne da ‘ya mace za ta samu zarafin fita tayi aikin da za a biya ta bayan wani lokaci. Budurwa, Bazawara da kuma Matar Aure sune idan ana maganar aikin mace za a Sanya su a ciki. A addinance duk mumini anaso yayi kishin iyalansa gwargwadon iko, amma wasu ba haka bane illa tunanin wani abu da zarge-zarge akan iyalansu. Wasu kuma matan basa iya kame kansu a duk lokacin da suka ga ba a ganinsu. Amfanin aiki ga ‘Ya mace sun hada da; Taimakawa alummarta, Taimakawa kanta, da Iyalinta, kara soyayya da kauna da sauransu. Zan iya barin matata tayi aiki amma bisa wasu sharuda da zan so a kiyaye. Kuma yin aikinta zai taimaka mana kwarai da gaske domin ko babu komai wasu abin musamman na yara kafin a tambayeni an yi wa yara abun da ya samu. Kuma ita kanta matar akwai bukatu nasu na mata da kafin na sani an yi wa kai da dai makamantansu. Ga misalin sharrudan; Kiyaye dokokin Allah, Tsayawa a matsayin da Allah ya ajiye ki, Girmama mijinki, Hakkin iyali (Yara da abokan zama). Za a iya jawo hankalin mazaje akansu sahalewa iyalansu musamamman masu ilmin yin aikin da su yi domin taimakawa al’umma da kuma tattalin arzikin kasa. Yin aikin na da mutukar amfani duba da yadda sauran al’umma ke barin kowanne jinsi a mutanensu da su yi aikin gwargwadon ilmin da Allah ya hore musu.
Mustafa Lawal Muhammad:
Idan Mace tana aiki an samun karamchin Tarbiyar ‘Ya’ya da rashin shakuwar ‘Ya’ya saboda rashin Lokacin ta garesu ita da Maigidanta. Aiki ba shi da amfani a gurin Mace musamman yadda take takama da gadara da girman kanta a gurin Mujinta da takamar tana da lasisin tana da ‘future’, idan ka sake ni wannan kenan. Hanyar da Mace take bi don shawo kan Mijinta ya barta tayi aiki shi ne; Rigima da Fitina da rashin Mutumci da fada a tsakanin Miji da ‘yan uwan Matarsa da kuma Bakin Talauchi da yake damun Miji bayan tara Ya’ya.
Abdullahi Muhammad daga Jihar Kano Gama:
Abun da ke saka maza basa barinsu fita aiki abu biyu ne a fahimta ta na daya al’ada na biyu kuma addini. Amfanin aiki ga ‘ya mace shi ne wajen harkar lafiya, maimakon namiji ya duba mace idan akwai mace likita sai ta duba ta. rashin amfaninsa shi ne rashin cikakken bawa miji da ‘ya’ya lokaci, musamman ga macen da ke aiki a banki, wa ta ma’aikata da ba ta lafiya ba. Ya danganta da wanne aiki ne za ta yi, zan iya barin matata tayi aikin da ya danganci lafiya ne kadai, amma sabanin haka ba zan barta ba. Shawara don fahimtar da mazan shi ne a saka su fahimci addini da abun da ya hana da abun da bai hana ba , sannan su karanci al’ada.
Aysha Maman Khadija daga Funtua, Jihar Katsina Nijeriya:
Da yawan mazan yanzu ba wai kishi ke hanasu barin matansu aiki ba, Kawai wani tunani ne na kadda wataran ta fisu, Allah kadai ya san adadin amfanin Aikin ‘ya mace a wannan zamanin da muke ciki, domin za ta taimaka kanta da ‘yan uwanta, sannan mijinta da yaran da za su haifa kafin aje kan sauran mutane, Aikin diya mace na matukar tallafawa musamman ta bangaren auratayya tun da idan tana da abun yi ba za ta taba tsayawa jiran kai ma ta ba balle har rai ya baci. Tabbas inda ni namiji ce zan iya barin matata tayi aiki sabida amfanin da za a samu da aikin nata, Sannan ban ga dalilin da zai sa in hanata yin aiki ba tun da har iyayen ta suka amince ma ta tai karatun. Amma idan ban da ra’ayin matata tai aiki to tabbas zan ba ta wani jari me kauri domin tayi sana’ar da za ta maye ma ta wannan gurbin na aiki dana hanata zuwa. Shawarar da zan ba da Ita ce, tauye hakki ne mace tayi karatu sannan ka hanata aiki, dan haka aikin nata kai zai fara temakawa kamin kowa, dan kuwa kafi kowa ya yi kusanci da ita lokacin, Idan ka bari matarka tai aiki Tabbas kayi jihadi kuma za ta taimaki kanta da yaranta da makusanta. Sannan sauran mutane, kuma za ka sami lada a duk lokacin da tai wani abun alheri dan za a ce matar wane ce shi ne ya bata damar yin aikin.
Mujittaba Ya’u Ali B/PRP Karamar Hukumar Nasarawa, Kano:
Kishi ne yake sawa mafiyawan maza ba sa barin matansu aiki wasu kuma suna gudun yayinda matansu suke aiki sai raini ya shiga tsakaninsu wadansu lokutan ma har da wulakanci. Aikin ‘ya mace nada mutukar mashimmanci saboda za ta taimakawa al’umma za kuma ta taimaki yaran ta ko da kuwa mujinta yanada dukiya kamar asibiti ko makaranta da kuma sauransu. Eh!in zan zan’iya barinta tai aikih saboda ta taimakawa kowa da kowa. Gaskiya ya kama maza su rage kishi saboda su ba da gudunmawarsu ga al’umma dan da akwai matsalar da sai mata za su fi saurin maganinta.