Kamar kowanne mako shafin Taskira ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, kamar; zamantakewa na rayuwar yau da kullum, zamantakewa tsakanin ma’aurata, rayuwar matasa, rayuwar soyayya, da dai sauransu.
Yau ma shafin na tafe da wani sabon tsokacin game da abin da ya shafi sabanin mu’amula tsakanin ‘Yan’uwantaka ko abota da dai sauransu.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kai Wa Ayarin El-Rufai Hari
- Raya Dangantaka Tsakanin Sin Da Rasha Zai Amfanawa Duniya Baki Daya
Sau tari a rayuwa akan samu kyakkyawar mu’amula tsakanin wasu mutanen daban, wadanda ba ‘yan`uwa na jini ba, haka ma tsakanin ‘yan`uwa na jini shakuwa na yawaita a koda yaushe, yayin da dayan ciki zai kasance mai yawaita alkhairi a kullum ga abokinsa ko dan uwansa. Sai dai kuma duk yawan alkhairin da dayan yake kokarin aikatawa a kullum, da zarar ya bata wa daya zance zai sha bamban, domin kuwa wanda aka bata wa zai hau dokin zuciya ne ya rinka fadar munanan kalamai akan wanda ya ke yawaita masa alkhairi a kullum. Wanda yawaitar afkuwar hakan cikin mutane, ke sa wasu jin tsoron zurfafa mu’amularsu ga kowa, da kuma nisantar mutane ko da kuwa za su kusanto su da alkhairi.
A kullum tunaninsu da hangensu baya wuce na karin maganar Malam Bahaushe da ya ke cewa; “Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta – shafawa naka ruwa”, a ganinsu ta hakn ne kadai za su iya maganin matsalar, tunda masu irin halin ba tukwane bane bare a kwankwasa. Ko me ya sa wasu mutanen da zarar sun sami sabani ga abokan mu’amula ko ‘yan uwa suke munanan kalamai akan dayan komai alkairin da ya saba yi a kullum? Mece ce ribar yin hakan ko akasinta? Ko wanne irin matsaloli hakan zai iya haifarwa? Idan kai ne ko ke ce hakan ya faru har zance ya iso kunnenki/ka wanne mataki za a dauka? Shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu, inda suka bayyana nasu ra’ayoyin kamar haka;
Sunana Musbahu Muhammad daga Gorondutse Jihar Kano:
Tsabar son rai ne da kuma kin gaskiya. Hakan ba shida wata riba, saboda yana haifar da lalacewar zumunci da rashin aminci a zamantakewa. Shawarata zan yanke mu’amala ko na rage Mu’amalata da duk eanda yayi min haka. Masu aikata haka su sani cewa mafi yawan lokaci son rai yana haifar da danasani, yana lalata zumunci, sannan yana haifar da rashin yarda a tsakanin al’umma.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi (Dr. Haibat) daga Jihar Kano:
A gaskiya wannan abu bai kamata ba kuma hakan ya kan iya haifar da fituna, ya iya sa mutum cikin wani tunanin cewa da ma tunda babu yarda a tsakaninsu, mu zama masu fadar alkhairinl a koda yoshe ko da sabani ya shiga tsakaninmu ko da namiji da namiji ne, ko mace da namiji musamman tsakanin saurayi da budurwa. A gaskiya irin wadanan kanana-kananan maganganun ba su da wani riba illa ya kawo rashin jituwa a tsakaninmu ko kuma a cikin unguwani da rashin ganin girman na gaba, haka abun ba dadi, amma a gaskiya zan nuna kamar ban sani ba, in bawa zuciyata hakuri saboda bai zama lallai ace iri-irinsu a fada a gaban mutun ba, Allah ya sa mu dace duniya wa lahira maza da mata mu yawaita fadan alkhairi a junamu ko dan gobe ya ranmu ya zama mai kyau, saboda duk abin da za ka fada ya kasance kana da hujja a hunnu ko mai yana tafiya da hujja da kuma gaskiya Allah ya sa mu dace.
Sunana Abubakar Muhammad Shehu daga Jihar Kano:
Mafi akasarin hakan yana yawan faruwa ne da samari ko akasin haka. Hakan babu wata riba kawai suna son aibata ‘yan uwansu ne sakamakon matsalar da suka samu, kuma a musulunce ma hakan babu kyau, cin mutuncin dan uwanka musulmi. Hakan yana haifar da matsala kamar gaba, daina ganin mutuncin juna. Matakin da zan dauka shi ne zan bi hanyoyin da addinin musulinci ya tanadar mana, Shawara ta a nan ita ce mu kiyaye mu rungumu ‘yan uwan mu musulmai saboda yin hakan zai bawa wasu damar cin mutuncin mu.
Sunana Safiyya Mustapha Mu’az:
Gaskiya hakan bai dace ba, dan kun yi rigima da mutum bai kamata ka koma gefe kana zaginsa ba, ko kana masa kazafi kala-kala dan kawai kun yi rigima da shi, wannan hauka ne da kuma rashin Ilimi, kuma wallahi ka damu da shi ne, shiyasa har kake zuwa wani wajen kayi maganarsa, kuma tun farko dama ba sansa kake yi ba, dan idan ace a baya kana sonsa to dan kun yi rigima da shi ba zai yiwu ka je wani gurin kana zaginsa ba, gaskiya hakan kuskure ne babba. Hakan ba shi da riba ko kadan, hasali ma suna daukarwa kansu zunubi ne sanadiyar gabar da suke yi da junansu, kuma sun san hukuncin duk mutumin da ke gaba da dan uwansa. Matsalar hakan idan family ne sun bata zumuntarsu kuma idan suna da yara suma haka za su taso cikin wannan halin da suka ga iyayensu nayi basu taba ganin girman wadancan ba, kuma ba za su taba son su ba. ba zan dauki ko wanne mataki ba tunda ni na san halina, kuma ba zan taba kullata ba, sabida idan na zauna ina kulata gaba daya za mu zama mahaukata, sannan kuma jahilai, dan haka zan zuba mata ido ta karaci haukanta da gulmace gulmacanta ita ta ga za ta iya. Shawara ta anan ga masu irin wannan halin su yi hakuri su daina, su gane shaidanne ke hadasu rigima da ‘yar uwarsa, kuma shaidan yana mutukar son hakan da suke yi, dan haka dan Allah ‘yan uwa mu rinka hakuri da junanmu, ka da mu bari shaidan yayi galaba a kan mu yakl koma gefe yana mana dariya.
Sunana Yakubu Obida Unguwar Farawa, karamar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano:
Abin da ya ke faruwa kuna tare da abokan hulda ba ka taba tunanin za su yi maka irin haka ba, to idan haka ta kasance sai ki ga mutum ya manta da duk alkhairin da kai masa a baya sai ki ga wannan abun da ya faru, a lokacin ya fi zafi hakan shi ya ke sa mutum ya manta alkhairinka na baya, saboda jin zafin abun da kuma tunanin ba za ka iya yi masa hakan ba. A gaskiya hakan ba shida riba kuma hakan zai iya janyo mummunan gaba, idan ba ayi kokari an sulhunta ba zai iya gangarowa har kan ‘ya’ya. Babu abun da mutum zai iya sai dai kawai ya barwa Allah. Dukkan masu irin wannan halin gaskiya ba abu bane me kyau ya kamata a gyara.
Sunana Zulkifilu Lawal (Naka Sai Naka):
Gaskiya me yin hakan bai dace ba, ya kamata idan mutum ya yi maka alkairi ka da ka manta komai kankantarsa, sannan wannan dabi’ar tana faruwa ne ga masu karancin ilimi, wasu lokutan su ne za su yi maka laifi, amman kuma su ne za su rinka fushi da kai. Gaskiya yin hakan ba shi da wata riba illah ma koma baya a rayuwa, mataki shi ne; mu dage da neman ilimi, sannan kuma mu yi aiki da shi, domin gudun fadawa halaka, sannan mu rage karbar amanar da muka san tafi karfinmu, shawara ita ce; in har ka san halin mutum bai kamata ka bashi wata damaba wadda matsala za ta shiga tsakaninku ba, ya kamata jama’a mu lura mu ya kiyaye domin wanzar da zaman lafiya da kaucewa fadawa fushin ubangiji, domin neman zaman lafiya tsakanin al’umma baki daya, Allah ya sa mu dace amin.
Sunana Mas’ud Saleh Dokadawa:
Raahin ba da kyakyawar shaida akan mutanan da aka tanada mun sabani da su don wani abu ya faru a baya, wannan shi ne tsananinin rashin adalci, kuma munafunci ne, ba wani dalili da ya ke sawa mutane suna yin hakan illa sharrin shedan, kuma rashin ilimi da rashin sanin mu’amala a shari’ance yana kawo haka. Ba shida wata riba, faduwa ce zallah saboda ba a yi wa juna adalci, hakan kuma bai kama da halayen musulmi na kwarai ba. Rashin zaman lafiya a zamantakewa, tabarbarewar zuri’a bayan mutuwa. Matakin da zan dauka na farko hakuri zan yi, sannan zan kyautata masa, kuma zan yi mu’amala da shi kyakyawa, sannan yawaita nasiha lokaci-lokaci. Shawarata na farko su ji tsoron Allah su daina, sannan su koma makaranta dan neman ilimi, hakan tsaban jahilci ne, kuma babu ya kamata a cikin abin, don bata mu’amala ne a tsarin zamantakewa.