Idan matasa suna da karfi, kasa ma za ta yi karfi. Matasan kasar Sin a wannan sabon zamani suna cikin lokaci mafi kyau na ciyar da al’ummar kasar Sin gaba. Baya ga kasancewar suna fuskantar damammaki da dama, a daya hannu suna kuma fuskantar manufar zamani wato “Sauke nauyin manyan ayyuka”.
Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya dora muhimmanci sosai kan ayyukan matasa, kuma a ko da yaushe, yana damuwa game da ci gaba da samun nasarar matasa.
Tun daga shekarar 2012, a kowane bikin matasa na ranar 4 ga watan Mayu, babban sakatare Xi Jinping, ya saba da mu’amala da tattaunawa da matasa, inda ya yi tsokaci cewa, ya dace su yi kokari domin cimma burinsu, kuma su yi aiki tukuru ba tare da bata lokaci ba. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp