Da take mayar da martani kan kalaman da ‘yan kasuwar Amurka game da rashin kafa doka kan “kudirin dokar iznin tsaron kasa” wanda ya haramta kasuwanci da masu kera sassa na’urorin laturoni na kasar Sin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, ra’ayoyin ‘yan kasuwan Amurka sun nuna cewa, tsoma baki da ake don lalata tsarin samar da kayayyakin masana’antu, bai dace da moriyar ko wane bangare ba, kuma bai samu karbuwa ko kadan. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)