Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ya bayyana cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da ta cimma da Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa. Shugabannin NLC sun amince da tayin ₦70,000 domin daƙile yiwuwar ƙarin farashin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke shirin yi. Da farko, ƙungiyar ƙwadagon ta nemi ƙarin albashi mafi girma, amma ta yanke shawarar yin rangwame domin kaucewa ƙara wahalar da ‘yan Nijeriya.
An cimma wannan matsaya ne bayan taron gaggawa na NEC da aka gudanar a Abuja, bayan wani taro da aka yi da Gwamnatin Tarayya a ranar 18 ga Yuli, 2024. Taron, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, ya haifar da tattaunawa mai zurfi wanda ya kai ga amincewa da albashi mafi ƙaranci na ₦70,000. Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, cikin wata sanarwa, ya yaba da jajircewar shugabannin ƙungiyar wajen gudanar da tattaunawar albashi.
- Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Tarayya Da Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Amince A Kan N70,000 Mafi Ƙarancin Albashi
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu Da Kashi 50 Cikin 100
NEC ta NLC ta amince da tayin Shugaban Ƙasa na ₦70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma wa’adin duba shi bayan shekaru uku. Sun kuma buƙaci cikakken bin dokar mafi ƙarancin albashi na ƙasa da zarar ta zama doka a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Duk da wannan amincewa mai wahala, NLC ta jaddada ƙudirinta na karewa da inganta hakkokin ma’aikatan Nijeriya, kuma ta kira ‘yan Nijeriya gaba ɗaya su haɗa kai wajen riƙe shugabanni kan alhakin irin wannan sadaukarwa da ta rataya a wuyansu.