• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsoro, Fargaba Da Wahala: ‘Bala’in Da Muka Gani A Yakin Sudan

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
in Kasashen Ketare
0
Tsoro, Fargaba Da Wahala: ‘Bala’in Da Muka Gani A Yakin Sudan
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Alawia Babiker Ahmed mai shekara 19 ta yi bari a lokacin da take gudu da kafa domin tsira daga kazamin yakin basasa da ya daidaita yankin Darfur na yammacin Sudan.

”Ina ta zubar da jini a kan hanya,” ta gaya wa BBC, kafin ta kara da cewa, ta ga ma mutanen da suka ma fi ta shiga tsaka-mai-wuya, wadanda yanayinsu ya fi nata a wannan lokaci da take tafiyar kwana uku ta nisan kilomita 70, cikin fargaba da tashin hankali daga birnin el-Fasher da aka yi wa kawanya zuwa dan karamin garin Tawila.

  • Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali
  • Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Alawia ta bayyana yadda ita da ‘yan’ uwanta suka ga wani dan karamin yaro yana kuka kusa da mahaifiyarsa wadda ta rasu tana yashe a gefen titi, a daidai lokacin da su kuma suke ta kauce wa hare-hare ta sama da ‘yanbindiga.

Alawia ta ce ta dauki yaron, ita kuwa gawar uwar suka rufe ta, suka ci gaba da tafiya.

Sudan ta fada bala’in yakin basasa tun bayan da fada ya barke tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun RSF, a watan Afirilu na 2023.

Labarai Masu Nasaba

An Tsare Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa

An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu.

Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin kasar da kawayenta.

Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke kokarin kama shi.

A watan Afirilu RSF din ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba kasar.

Alawia ta ce yayin da fadan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita da mutanen gidansu suka tsere a kafa zuwa Tawila da ke yamma da el-Fasher.

‘Ya’yanta Marwan Mohamed Adam, mai shekara 21, ya gaya wa BBC cewa mayakan da ke da alaka da RSF sun ci zarafinsa a hanya inda suka lallasa shi da duka, har suka yi masa fashin ‘yan abubuwan da yake dauke da su.

Marwan ya ce ya tsira daga hannun gungun ne saboda ya yi musu karya daga inda ya fito.

Ya ce maharan sun debe matasan da suka gaya musu cewa daga el-Fasher suke suka je suka harbe su.

”Saboda haka a lokacin da suke yi min tambayoyi na ce musu daga Shakra nake – wanda zango ne a kan hanyar zuwa Tawila,” in ji shi.

“Za ka ji tsoro da fargaba, kana cikin tashin hankali, ka ji kamar ma ka riga ka mutu,” in ji Marwan mai shekara 21, a hirarsa da BBC, inda ya kara da cewa ya ga gawawwaki uku a kan hanya.

Wata matar, Khadija Ismail Ali, ta gaya wa BBC cewa “ga gawawwaki nan yashe a titi.”

Ta ce an kashe mutum 11 ‘yan gidansu a lokacin da ake yi wa el-Fasher ruwan makamai ta sama, kuma kananan yara uku sun mutum a lokacin tattakin da suka yi na kwana hudu daga birnin zuwa Tawila.

“Yaran sun rasu ne sakamakon kishirwa a hanya,” in ji Khadija.

‘Yanbindiga masu alaka da dakarun RSF sun kai hari kan kauyen iyalinta, el-Tarkuniya, a watan Satumba da ya wuce, inda kuma suka sace musu amfanin gona.

A lokacin suka tsere zuwa sansanin Zamzam inda ake fama da yunwa, daga nan kuma suka kara gaba zuwa el-Fasher yanzu kuma zuwa Tawila.

Kungiyar bayar da agajin lafiya – Alima ta ce ‘yanbindiga sun kwace filaye da gonakin yawancin iyalai a lokacin da suka kai musu hari.

Kungiyar ta kara da cewa wadanda suke zuwa Tawila, yawanci yara tuni sun kamu da cutar tsananin yunwa.

Alawia ta ce ‘yar uwarta ta jefar da dan abincin da suka yi guziri a lokacin da suke neman tsira daga hare-haren sama da suka gamu da su bayan sun wuce Shakra.

“Dan wani guntun wake ne da ya rage da dan gishiri muka rike a hannunmu domin ciyar da yara,” ta ce. Haka suke ta tattaki ba tare da ruwa ko abinci ba, har suka hadu da wata mata da ta ce musu za su iya samun ruwa a wani kauye da ke kusa.

Tawagar tasu ta tashi cikin dare domin ci gaba da tafiya zuwa wannan kauye, to amma ba su san cewa ashe suna yanki ne da ke karkashin ikon mayakan RSF ba.

“Mun gaishe su, amma kuma ba su amsa mana ba. Sun umarce mu, mu zauna a kasa, suka bincike kayanmu,” in ji Alawia.

Mayakan sun karbe kudin da muke rike da su fan 20,000 (na Sudan) (daidai da Dala 33), gaba daya kudin da iyalan ke da shi, tare da tufafi da takalman da suke dauke da su.

“Takalmana ba su da kyau amma duk da haka suka kwace su,” in ji Alawia.

Ta kara da cewa mayakan RSF sun ki su ba su ruwa, saboda haka suka ci gaba da tafiya har sai da suka kai kauyen el-Koweim.

A can suka hangi wata rijiya da mayakan RSF ke tsare da ita.

“Mun roke su, su ba mu ruwa akalla ko don yaron nan maraya, amma suka ki,” in ji Alawia.

Ta kara da cewa ta matsa domin ta je rijiyar amma mayakan suka mangare ta.

Iyalan sun ci gaba da tafiya haka a galabaice cikin kishirwa har sai da suka kai Tawila, inda isar su ke da wuya sai Alawia ta zube kasa, nan da nan aka garzaya da iya asibiti.

An sallame ta bayan an yi mata magani.

Haka shi ma yayanta Marwan an yi masa maganin raunukan da ya ji a lokacin da mayakan suka yi masa duka.

Alawia ta ce daga nan ne suka shiga neman dangin wannan yaron da suka ceto, bayan sun same su, suka danka musu shi.

A yanzu Alawia da iyalanta na zaune a Tawila, inda wasu iyalai suka karbe su, suka ba su masauki a gidansu.

“Yanzu dai rayuwa mun gode wa Allah, amma muna da fargabar yadda za ta iya kasancew

a a nan gaba,” Alawia ta shaida wa BBC.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Sudan
ShareTweetSendShare
Previous Post

Bayern Munich Ta Fara Zawarcin Marcus Rashford

Next Post

Chelsea Ta Kammala ÆŠaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund

Related

An Tsare Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa
Kasashen Ketare

An Tsare Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Cin Hanci Da Rashawa

3 days ago
An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati
Kasashen Ketare

An Kama Tsohon Firaministan Mali Bisa Zargin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

1 week ago
Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka
Kasashen Ketare

Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka

2 weeks ago
Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?
Kasashen Ketare

Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu?

3 weeks ago
Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
Kasashen Ketare

Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa

3 weeks ago
Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza
Kasashen Ketare

Faransa Za Ta Fara Jefa Kayan Agaji Ta Sama A Gaza

3 weeks ago
Next Post
Chelsea Ta Kammala ÆŠaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund

Chelsea Ta Kammala ÆŠaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

August 23, 2025
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

August 23, 2025
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

August 23, 2025
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

August 23, 2025
Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

August 23, 2025
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kama Waɗanda Suka Kashe Masallata A Malumfashi 

August 23, 2025
Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

August 23, 2025
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

August 23, 2025
2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe

2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe

August 23, 2025
Zaben Cike Gurbi: Tinubu Ya Lalata Tsarin Zaben Nijeriya — ADC

Zaben Cike Gurbi: Tinubu Ya Lalata Tsarin Zaben Nijeriya — ADC

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.