Wasu tubabbun mayakan Boko Haram 13 da aka horar da su aka kuma aka sanya su cikin jami’an da ke taimaka wa sojojin da ke aiki a Jihar, sun tsere da babura da makaman da aka ba su.
Rahotanni sun bayyana cewar mayakan 13 na daga cikin daruruwan mutanen da suka ajiye makamansu.
- Mutane 7 Sun Mutu, 10 Na Kwance A Asibiti Sakamakon Ɓarkewar Cutar Kwalara A Kano
- Tallafin Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Buƙaci Gwamnatin Sakkwato Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Biliyan Uku
Wani mai bincike, Samuel Malik, ya bayyana cewar mayakan 13 na yaki ne tare da sojoji a karamar hukumar Mafa da ke Jihar Borno.
Jami’in ya ce bayan tserewar su, sun nadi bidiyo inda suke nuna makaman da suka tsere da su.
Tun bayan da sojin Nijeriya suka fara nasarar murkushe Boko Haram a 2015, mayakan suka fara ajiye makamansu.