Kungiyar kwadago (NLC) ta kasa reshan Jihar Kano, ta bayyana cewa tun a shekarar 2003 zuwa yau bashin ‘yan fanshon Kano ke bin gwamnati ya taro zuwa Naira billiyan 69 da milliyan 200.
Kungiyar karkashin Shugabancin Kwamared Kabiru Ado Munjibir, ta jagoranci kungiyar ‘yan fanshon wajen yin zanga-zangar lumana na tuna wa gwamnatin halin da ‘yan fashon Kano suke ciki, domin warware wannan matsala.
Shugaban kungiyar NLC na Kano bayyan hakan ne lokacin kammala takaitaciyar zanga-zangar da aka fara daga gidan Sarkin Kano da ke Nassarawa zuwa gidan gwamnatin Kano a ranar Alhamis da ta gabata.
Har ila yau, shugaban NLC ya ce wannan bashi da ‘yan shansho suke bi ba wai iya wannan gwamnatin ta yanzu ne abun ya fara ba, ya fara ne tun daga kan gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau da ta fara a 2003 zuwa 2011 ba ta gama biyan duk hakkin ‘yan fashon ba duk da kokarin da ta yi, haka ita ma gwamnatin Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ita ma haka ta bar ragowa hakkin ‘yan fashon, to sai kuma wannan gwamnati da ta zo a 2015 wadanan makudan kudade har billiyan 69 gwamnatocin Kano uku ne suka tarashi da ake neman yanzu gwamnati ta biya su kamar yadda doka da tsara.