UADD ta yaba wa Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation (SABMF) bisa jajircewa da himma da kishin kasa, bisa kiran muhimmin taron kwanaki biyu na hadin gwiwar da aka gudanar a Arewa House, da ke Kaduna daga ranar ranar Talata 29 ga Yuli zuwa Laraba 30 ga Yulin 2025.
UADD ta yaba wa gidauniyar kan kokarinta na samar da wani dandali da zai samar da hulda kai tsaye tsakanin masu ruwa da tsaki na arewa da manyan jami’ai masu rike da madafun iko na gwamnatin tarayya, lamarin da aka bayyana a matsayin wani gagarumin ci gaba wajen tabbatar da gaskiya da hadin kan ‘yan kasa.
- Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya
- Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho
Kungiyar ta kuma yaba wa shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa tabbtar da
dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron.
“Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane
Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya.
Mahalarta taron sun hada da; Sakataren Gwamnati na Tarayya, Sanata George Akume, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Christopher Musa, Hafsan Hafsan Sojin Sama Hassan Bala, Kwamanda Janar na NSCDC Dr. Ahmed Abubakar Audi, Shugaban Gwamnonin Arewa, Mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara Da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Hon. Abdulrazak Abdulrahman, Wanda Ya Wakilci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR duk hallara a wurin taron. Sauran sun hada da Mashawarciya ta Musamman ga shugaban kasa akan harkokin siyasa, Hadiza Bala Usman, da sauran shugabani da hukumomi daga yankin.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinentan UADD Kwamared Jamil Bala Muhammad, ta ce, zaman tattaunawa ya bai wa Arewa damar yin tunani akan ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma gabatar da ra’ayoyi na gaskiya.
Kazalika, UADD ta yaba wa Babban Darakta Janar na tunawa da Sir Ahmadu Bello Foundation, Engr. Abubakar Gambo Umar bisa hangen nesa da jajircewar sa. In ji sanarwar.
Manyan abubuwan da aka mayar da hankali kansu sun hada da yabon gwamnatin Tinubu kan nasarori da kokarin da ta yi a bayyane don cika alkawuran da aka dauka yayin yakin nenam zave, musamman a harkokin tsaro da sake fasalin tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp