Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana kyautar kujerar aikin Hajji ga zakarun (Mace da Namiji) da suka lashe musabakar karatun Alkur’ani ta shekara-shekara a jihar Kaduna.
Gwamnan wanda ya halarci rufe musabakar a filin musabaka na Dr. Ahmad Muhammad makarfi quranic recitation complex, kinkinau/’yantukwane, Kaduna a ranar Asabar ya kuma bayar da kyautar kudi ga wadanda suka lashe gasar daga matsayi na daya zuwa na biyar a rukuni daban-daban na gasar.
- Minista Ya Biya Tarar Naira Miliyan 585 Domin A Saki Daurarru 4,068
- Sojoji Da ‘Yan banga Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
Da yake karin haske game da aikin Hajji na 2024, Gwamnan ya ce, ya kaddamar da kwamitin da zai tabbatar da cewa, aikin Hajjin badi bai fuska kalubale ba kamar yadda na bara ya ci karo da kalubale daban-daban. Alhazai sun gamu da damuwa daga bangaren abinci, masaukai da sauransu.
Ya yi nuni da cewa, mutane da dama sun tuntube shi domin neman kwangilar ayyukan aikin Hajji kamar kayan sawar alhazai da abinci da wurin kwana da sauransu.
“Abin da nake so na gaya wa duk wanda ya samu kwangilar aikin Hajji, shi ne ya ji tsoron Allah, kuma ya bai wa alhazai abin da ya dace domin su samu kyawawan addu’o’in alhazai ba na fushinsu ba. ” in ji shi.
Yayin da yake magana kan mahimmancin Alkur’ani mai girma, Gwamna Sani ya ce, al’umma za su samu zaman lafiya idan dukkan musulmi suka rika karanta Alkur’ani a kai a kai tare da bin koyarwarsa, ya ce za a magance yawancin kalubalen da ake fuskanta a kasar nan.
Tunda farko, da yake gabatar da fadakarwa a wajen taron, Jagoran kungiyar Jama’atu Izalatu Bid’ah Wa Ikamatu Sunnah (JIBWIS) ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce, Alkur’ani shi ne wanda duk al’ummar musulmi ta tafi akai kuma bata da wani bambancin ra’ayi akansa.
Don haka, ya bukaci al’ummar musulmi musamman malamai da su koma ga Alkur’ani su karantar da shi ga sauran jama’a, yana mai cewa, itace hanya mai sauki wajen dorewar zaman lafiya.