An yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa inganta tsarin ilimi a jihar ta hanyar amfani da sabbin fasahohi da dabaru masu amfanarwa.
Wannan yabo ya fito ne daga babbar sakatariyar hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Hajiya Aisha Garba, yayin wata ziyarar aiki da gwamna Malam Umar Namadi ya kai hedikwatar UBEC da ke Abuja ranar Laraba.
- ‘Yansanda Sun Cafke Ƙasurguman Masu Garkuwa Da Mutane 2 A Yobe
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 10, Sun Kashe Ɗan Bindiga 1 A Katsina
A cewar Hajiya Aisha, Jihar Jigawa a karkashin jagorancin Gwamna Namadi, ta gina ajujuwa fiye da 3,000, ofisoshi 30, rijiyoyin burtsatse 500, bandakuna 1,200, ta raba kujeru 1,250, tare da horas da malamai fiye da 17,000.
Wadannan ayyuka domin inganta harkar ilimi da kuma nuna gaskiya, sun sa Jigawa ta zama abin koyi ga sauran jihohi.
Tunda farko, Gwamna Malam Umar Namadi, a nasa jawabin, ya ce gwamnati ta dauki kwakkwaran matakai na magance matsalar rashin ilimi bayan wani bincike da wani masani mai zaman kansa ya fitar cewa, yawancin daliban firamare ba su iya karatu ko rubutu yadda ya kamata.
Ya bayyana cewa, an dauki malamai sama da 7,000 a karkashin gwamnatinsa domin karfafa ilimin boko, ya kuma ce jihar ta bullo da sabbin dabaru da suka shafi al’umma, kamar taron iyaye mata da kuma farfado da kwamitocin gudanarwa na makarantu (SBMC), domin inganta zuwan yara makarantu da kuma lura da yadda malamai suke aiki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp