Kylian Mbappe ya zira kwallo a raga yayin da Paris St-Germain ta zama ta daya a rukunin F bayan da ta doke AC Milan a gasar zakarun Turai.
Mai masaukin baki yanzu maki biyu tsakaninita da Borussia Dortmund, wadanda suka doke Newcastle da ci 1-0 ranar Laraba.
- UEFA Champions League: Abinda Ya Kamata Ku Sani Akan Wasan Real Madrid Da Napoli
- Pedri Ba Zai Buga El-Clasico Ba Saboda Rauni
Mbappe ne ya fara zura kwallo a ragar Milan a minti na 32 da fara wasa.
Kuma kwallayen da Randal Kolo Muani da Lee Kang-in suka zura a ragar ne suka tabbatar da dukkanin maki uku ga zakarun na kasar Faransa.
Milan ta ci gaba da zama a matsayin wadda ba ta yi nasara ba a gasar zakarun Turai a bana,inda take matsayi na karshe a rukunin F, da maki biyu a wasanni uku na farko.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp