A daren yau Talata za a fara fafatawa a gasar zakarun turai (UEFA Champions League), inda kungiyoyi da dama za su kara da juna.
Mai rike da kambun Real Madrid ta yi tattaki zuwa gidan Celtic inda za su barje gumi a gasar.
- Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 5, Ya Lalata Gidaje 3,813 A Katsina
- Magidanci Ya Nemi Matarsa Ta Biya Naira Miliyan 1.6 Kafin Ya Sake Ta A Kaduna
Real Madrid ce ta lashe gasar ta 2021/2022 bayan doke Liverpool da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar.
Hakan ya bai wa Real Madrid damar lashe gasar karo na 14 a tarihinta, kuma zama kungiyar da ta fi kowace lashe gasar.
Manyan kungiyoyi irinsu PSG, Real Madrid, Barcelona, Manchester City, Chelsea, Juventus, Bayern Munich da sauransu za su fafata a gasar a tsakanin yau zuwa gobe Laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp